--
Kada ka raga wa kowa: Huɗubar Ganduje ga shugaban hukumar yaƙi da rashawa ta Kano

Kada ka raga wa kowa: Huɗubar Ganduje ga shugaban hukumar yaƙi da rashawa ta Kano

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya faɗa wa shugaban hukumar sauraron ƙorafin jama'a da yaƙi da rashawa ta jihar, Muhyi Rimingado ya yi aikinsa ba tare da sani ko sabo ba. Ganduje ya kuma fada wa Ramingado kada ya ɗaga wa kowa ƙafa wurin yaƙi da rashawa ko da ƴan fadar gwamna ne. 

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da ya kai ziyara hedkwatar hukumar a ranar Asabar domin duba aikin gyara da kwaskwarima da ake yi. 

A cewar Ganduje, ba zai yi wu gwamnatin tarayya ita kaɗai ta yi yaƙi da rashawa ba idan jihohi ba za su yi yaƙi da rashawar ba suma. "Duk wanda ya faɗa tarkon hukumar zai fuskanci hukunci. Ba ruwa na. Ba zan saka baki ba koda wanene. Saboda haka kada ka ɗaga wa kowa ƙafa ko da ƴan fada na ne," a cewar Ganduje. 

Ya ƙara da cewa, "Yadda masu rashawa ke ƙoƙarin daƙile ƙoƙarin hukumomin rashawa, kuma kasancewar yaƙi da rashawa ɗaya daga cikin abubuwan da gwamnatin Shugaba Buhari ta saka a gaba, gwamantin tarayya ita kaɗai ba za ta iya ba, dole sai jihohi sun shiga za a samu nasara." 

Da ya ke jawabin buɗe taron tunda farko, Ramingado ya yaba wa ƙoƙarin Ganduje wurin yaƙi da rashawa a jihar inda ya ce," jajircewar ka da goyon baya ne yasa hukumar mu ke cikin wadanda suka fi inganci a jihar." 

"Mun zama abin koyi ga wasu jihohi a kasar nan," in ji shi. Idan za a iya tunawa, a cikin ƴan kwanakin nan hukumar ta kwato wasu kudade da aka ware domin masu addu'o'i da wani hadimin gwamnan ya handame. 


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Kada ka raga wa kowa: Huɗubar Ganduje ga shugaban hukumar yaƙi da rashawa ta Kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?