LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Jirgi Majalisar Dinkin Duniya ya yi hatsari dauke da albashin ma'aikata a Sudan ta Kudu

Jirgin kwasan kaya na Majalisar Dinkin Duniya ya yi hatsari bayan ya dauko albashin ma'aikatan hukumar samar da abinci ta Majalisar - Mutane tara ne ke a cikin jirgin lokacin afkuwar lamarin, takwas daga ciki sun mutu 

Har ila yau albashin ma'aikatan kimanin dalar Amurka 35,000, sama da miliyan 16 kenan a kudin Najeriya ya kone kurmus Rahotanni da muke samu ya nuna cewa wani jirgin kwasan kaya na Majalisar Dinkin Duniya ya yi hatsari bayan ya dauko albashin ma'aikatan hukumar samar da abinci ta Majalisar, sashin Hausa na BBC ta ruwaito. 

An tattaro cewa irgin ya yi hatsari ne a kusa da Juba, babban birnin Sudan ta Kudu. Kuma mutane tara ne ke a cikin jirgin lokacin afkuwar lamarin, takwas daga ciki sun mutu. Hatsarin ya afku ne a ranar Asabar, 22 ga watan Agusta. 

Mutum hudu daga cikin mutanen da suka mutu a hatsarin 'yan kasar Sudan ne, biyu kuma daga Tajikistan, yayinda dayan kuma ya kasance daga kasar Ukraine. Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir ne ya bayyana hakan a cikin wani sakon ta'aziyya da ya fitar. Mutumin da ya rayu na asibiti ana duba lafiyarsa. 

An tattaro cewa Bankin Opportunity Bank ne ya yi hayar jirgin domin kai albashin ma'aikatan hukumar WFP da ke a birnin Wau a Sudan ta Kudu. 

Ministan sufuri na kasar ya bayyana cewa kudin da jirgin ya dauko sun kone kurmus inda aka yi asarar kusan dalar Amurka 35,000, sama da miliyan 16 kenan a kudin Najeriya. 


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments