--
Yanzu Yanzu: Kwararren makashi Shodipe ya sake shiga hannu bayan saka kyautar kudi ga wanda ya fallasa shi

Yanzu Yanzu: Kwararren makashi Shodipe ya sake shiga hannu bayan saka kyautar kudi ga wanda ya fallasa shi

Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta sake kama wani shahararren makashi, Sunday Shodipe. Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Gbenga Fadeyi ya tabbatar da ci gaban ga Channels TV a ranar Lahadi, 23 ga watan Agusta. 

Mista Fadeyi bai bayar da cikakken bayani kan inda aka ajiye wanda ake zargin ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton. Kamun nashi na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan ya tsere daga hannun ‘yan sanda a ofishinsu na Mokola da ke Ibadan. 

‘Yan sanda sun kaddamar da neman Shodipe, wanda aka ce yana da hannu a kisa daban-daban da aka yi a karamar hukumar Akinyele na jihar, ruwa a jallo. 

Jami’an tsaron sun kama matashin mai shekaru 19 sannan suka gurfanar dashi tare da wasu mutum biyu a ranar 19 ga watan Yuli, a ofishin rundunar ‘yan sandan jihar da ke Oyo. A baya mun kawo maku cewa rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta sanar da saka kyautar N500,000 ga duk wanda ke da gamsasshen bayani abin dogaro da zai yi sanadiyar sake kama Sunday Shodipe, wani madugun mai kashe mutane. 

‘Yan sanda sun kama mai laifin a watan Yuli sannan aka adana shi a ofishin ‘yan sandan Mokola, amma sai ya tsere daga inda aka tsare shi a ranar 11 ga watan Agusta. Tserewar Shodipe ya haddasa cece-kuce da zanga-zanga a kan rashin kwarewar rundunar ‘yan sandan da ya tsare a karkashin kulawarsu.

Nwachukwu Enwonwu, kwamishinan ‘yan sandan jihar, ya daura laifin tserewarsa a kan wani jami’in dan sanda da ke hutun aiki. A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, Fadeyi Olugbenga, kakakin ‘yan sandan jihar, 

ya ce Enwonwu ya sanar da bayar da kyautar N500,000 ga duk wanda ke da bayani da zai taimaka wajen sake kama mai laifin. Ya ce duk wanda ya san maboyar mai laifin ya sanar da ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma ya tuntubi rundunar ta layukan da aka amince da su, jaridar The Cable ta ruwaito. 

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu Yanzu: Kwararren makashi Shodipe ya sake shiga hannu bayan saka kyautar kudi ga wanda ya fallasa shi "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?