LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Dumu-dumu: Yadda aka kama matasa biyu suna luwadi da junansu

Mazauna kauyen Agwete da ke birnin Kakamega na kasar Kenya sun lakadawa wasu matasa biyu mugun duka bayan sun kama su suna luwadi - Kamar yadda jama'ar yankin suka tabbatar, Wayenso, daya daga cikin matasan, sun tabbatar da cewa ya saba lalata yaran jama'a

Shugaban 'yan sandan yankin ya bayyana cewa, sun ceci matasan inda suka adana su a ofishinsu har zuwa lokacin da za a kammala bincike a kan lamarin Mazauna kauyen Agwete da ke garin Kakamega na kasar Kenya a ranar Juma'a da safe sun kama wasu matasa biyu a yayin da suke luwadi. 

Shugaban kungiyar dattawan yankin mai suna Nyumbi Kumi, Reuben Otiende, ya bayyana cewa sun dade suna zargin daya daga cikin matasan mai suna Wanyeso Alias Gili, da zama dan luwadin. An taba kama shi yayin da ya lalata wani yaron makwabcinsu, shafin Linda Ikeji ya wallafa. Mazaunan yankin sun balle kofar Wanyeso bayan sun ga wani matashi wanda ba dan yankin ba mai suna Caleb Andani, ya shiga gidansa.

An kama matasan biyu dumu-dumu yayin da suke luwadin kuma jama'ar yankin sun lakada musu mugun duka kafin zuwan 'yan sanda.

K2TV ta ruwaito cewa, Wanyeso bazawari ne wanda ya saki matarsa mai suna Grace Khavesta a shekarar da ta gabata. Allah ya albarkaci auren nasu da 'ya'ya uku kafin daga bisani su rabu. Wani makabcinsa ya ce, "Wanyeso ya saki matarsa ne ta yadda zai ci karensa babu babbaka ta hanyar yin luwadin da ya saba." 

Wani mazaunin yankin ya ce, "Muna kira ga mai gidan hayar da Wanyeso yake ciki da ya fattakesa saboda ba zamu ci da zama da dan luwadi a yankinmu ba. Wadannan ne mutanen da ke lalata mana yara." Shugaban 'yan sandan Kakamega ta tsakiya, 

David Kabena, ya bayyana cewa wadanda ake zargin za a gurfanar da su bayan an kammala bincike. Ba yau matsalar luwadi ke addabar al'umma ba. A kwanakin baya an kama wani mutum wanda ake zargi da lalata yara 12 a jihar Sokoto. 

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

 

Post a comment

0 Comments