--
Duba  yanda Sojoji sukayi juyin mulki a Mali suka kama shugaban kasar

Duba yanda Sojoji sukayi juyin mulki a Mali suka kama shugaban kasar

Sojoji masu juyin mulki a kasar Mali sun tsare Shugaba Ibrahim Boubakar Keïta bayan kwace iko a kasar.


Wani Kakakin gwamnatin kasar ya ce sojojin da suka yi ta harbe-harbe sun kuma yi awon gaba da Firaminista Boubou Cissé duk da cewa a baya ya yi kira da a yi tattaunawa ta fahimta.


Yunkurin juyin mulkin ya fara ne a safiyar Talata inda sojojin suka yi ta harbe-harbe a wani sansani a garin Kati da ke kusa da Bamako, babban birnin kasar.


A ranar ce kuma gungun wasu matasa masu zanga-zanga suka cinna wa gine-ginen gwamnati wuta a yayin zakaga-zangar kin jinin gwamnati a Bamako.


Gabanin nan sojoji sun tayar da tarzoma a babban barikin na Kati inda suka kame tare da kukkulle manyan hafsoshi a kwamandojinsu suka kwace iko.


Tuni dai Tarayyar Afrika da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS) da kasar Faransa da ta yi wa Mali mulkin mallaka suka la’anci juyin mulkin.


Matakin da sojojin kasar suka dauka ya zo ne a yayin da ake ta gangamin gudanar da zanga-zangar neman Shugaba Keita ya yi murabus.


‘Yan kasar na zargin shugaban da gaza magance matsalar tsaro da durkushewar tattalin arziki baya ga yawaitar cin hanci da rashawa.


SOURCE: AMINIYA DAILY TRUST

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Duba yanda Sojoji sukayi juyin mulki a Mali suka kama shugaban kasar"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?