LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Da izinin mahaifinsu na dinga musu fyade har suka yi ciki - Wanda ake zargi

Jami’an 'yan sandan jihar Legas ta damke wani matashi mai shekaru 28 kan laifin yi wa wasu matasan mata biyu fyade da ciki - Sai dai saurayin ya ce da izinin mahaifinsu yayi wannan aika-aikar

An damko mahaifin yaran saboda ya shiga cikin wadanda ake zargi Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta sanar da kamen wani matashi mai shekaru 28 da tayi a kan laifin yi wa wasu ‘yan mata biyu fyade da ciki.

Kamar yadda saurayin ya sanar, ya ce da izinin mahaifinsu yayi wannan aika-aikar. Majiyar daga ofishin 'yan sanda da ke Ikotun, wacce kuma al'amarin ke hannunta, ta zargi cewa Nduka Anyanwu ya dade yana lalata da yarinya mai shekaru 13 tare da yayarta mai shekaru 17.

Hakan ya fara faruwa ne tun suna makarantun firamare. Masu tuhuma a ofishin 'yan sandan sun sanar da Daily Trust cewa Anyanwu, wanda ke lalata da yaran ya ce da izinin mahaifinsu mai suna Christian Onyechi yake hakan.

An kama wanda ake zargin a jiya bayan gwajin da mahaifiyar yaran ta matsa a yi musu ya nuna suna dauke da ciki. 'Yan sandan sun ce yaran sun sanar da su cewa Anyanwu ya dade yana cin zarafinsu tun suna makarantar firamare.

An damko mahaifin yaran saboda ya shiga cikin wadanda ake zargi. Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Bala Elkana ya gagara, don baya daukar waya kuma bai yi martani a kan sakon da aka tura masa ba.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments