--
An kama Mai gari da zargin taimakawa masu satar mutane da mota a Imo

An kama Mai gari da zargin taimakawa masu satar mutane da mota a Imo

Wani mai sarautar gargajiya a kasar Uba a garin Awara, karamar hukumar Ohaji/Egbema da ke jihar Imo ya shiga hannun jami’an tsaro da zargin aikata barna. ‘Yan Sanda sun kama mai martaba Eze Andrew Okuegbunuwa da sunan cewa ana zargin sa da hannu wajen kitsa garkuwa da mutane da ake yi a yankin kasarsa da kewaye.


Jaridar Daily Trust ta ce ana zargin wannan basarake da agazawa wajen fashi da makami. A jiya Litinin ne jami’an ‘yan sanda su ka gabatar da wadanda ake zargin. Sauran wadanda su ka shiga ragar jami’an tsaron sun hada da wani likitan gargajiya da mutanen da aka samu dumu-dumu a wannan danyen aiki na sace mutane da dukiya.


Da yake yi wa ‘yan jarida jawabi a garin Owerri wajen gabatar da wadanda aka kama, Kwamishinan ‘yan sanda na Imo, Isaac Akinmoyede ya ce: “A ranar 28 ga watan Yulin 2020, da kimanin karfe 2:00 na rana ne dakarun SARS su ka yi nasarar cafke wani mutumi Eze Andrew Okuegbunuwa mai shekaru 59 da ke garin Awara,

karamar hukumar Ohaji/Egbema a jihar Imo, da hannu wajen laifin garkuwa da mutane da sauran laifuffukan fashi da makami.”

“Bincike ya nuna cewa wanda aka kama watau Andrew Okuegbunuwa ya ba masu garkuwa da mutane gudumuwar motar aiki, kirar jif ta samufurin Lexus RX330 mai lamba URM 404 EL.” “Bayan sun rasa motar a wajen ta’asarsu, masu garkuwa da mutanen sun ba Andrew (Okuegbunuwa) kudi N3, 000, 000 domin ya saye wata motar.”

Inji CP Akinmoyede. Kwamishinan ‘yan sandan ya kara da cewa: “An gano cewa wannan mota ba ta da takardun rajista a hukumar FRSC ta kasa.” A sanadiyyar damke mai martaban da aka yi, an yi nasarar kai ga wani Bernard Uzoma wanda ke taimakawa miyagun da magangunan gargajiya da za su yi masu maganin bacin rana. Jami’an tsaron sun karbo N4, 200, 000 daga hannun wadannan masu garkuwa da mutane da wasu N200, 000 da aka biya Bernard Uzoma.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "An kama Mai gari da zargin taimakawa masu satar mutane da mota a Imo"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?