--
Coronavirus a Kaduna: Elrufa'i ya ce watakila zai sake rufe jihar

Coronavirus a Kaduna: Elrufa'i ya ce watakila zai sake rufe jihar



Gwamnatin Kaduna ta ce tana duba yiwuwar sake rufe jihar saboda tashin alƙaluman mutanen da cutar korona ke kamawa a baya-bayan nan, "saboda mutane ba sa bin doka".

Yayin zantawa ta musamman da BBC, Gwamna Nasir Elrufa'i ya bayyana fargabar kada ƙaruwar annobar ta fi ƙarfin asibitocin Kaduna bisa la'akari da ganin yadda ƙwayar cutar ke ƙara bazuwa.

Alƙaluman da hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ke fitarwa a kullum sun bayyana gano masu cutar korona 54 ranar Juma'ar da ta gabata.

"Ranar Juma'a za ka ga mutane sun yi cunkoso, to, idan muka ce za mu buɗe masallatan khamsus salawat wannan cunkoso za a ci gaba da shi, ba a bin doka, ba a bin tsare-tsare," in ji gwamna.

A cikin kwana uku na baya-bayan nan kaɗai, cutar korona ta kama mutum 95 a jihar Kaduna, kamar yadda ƙididdigar NCDC ta nuna.

Duk ƙa'idojin da muka bayar wa'nda ya kamata a bi, yawancin mutane ba sa bi. Yau in ka buɗe kasuwa, mutum ɗaya in yana da wannan ciwo (irin) yadda ake cunkoso, zai iya ba mutane dubbai, cewar Elrufa'i.

Ya ƙara cewa: "Kuma da yake a kasuwa ne, im ma ka same shi, ka ga yana da ciwon, kana neman wa'yanda za ka jawo ka gwada su, ko sun samu ciwon, a kasuwa ina mutum zai san da wa, da wa ya haɗu?"

Haka kuma gwamnan ya koka kan yadda mutane ke ci gaba da rashin mutunta ƙa'idojin ba da tazara a wuraren ibada.

A baya dai, gwamnatin Kaduna ta sa dokar kulle fiye da tsawon wata uku kafin buɗe ta kuma yanzu haka jihar ita ce ta takwas a jadawalin jihohin Najeriya masu fama da cutar korona.

Sai dai har yanzu gwamnati ba ta buɗe wasu wuraren ibada da kasuwanni ba kamar a makwabtan jihar, abin da ya sanya mazaunan Kaduna ciki har da 'yan kasuwa kokawa.

Elrufa'i dai ya ce maimakon ci gaba da buɗewa ma, ƙila su sake rufe Kaduna, "a ma koma gidan jiya domin mutane ba su bin doka".



'Gara yin bara da mutuwa'

Gwamnan dai ya shafe kusan wata guda yana jinyar cutar korona bayan ya kamu a ƙarshen watan Maris, kafin sanar da warkewarsa daga bisani.

Ya ce gwamnati ta umarci mutane su riƙa sanya takunkumi a duk lokacin da suka fito daga gida, "amma mutane sun ƙi ji".

Yanzu in ka fita kana garin Kaduna, mun ce duk wanda ya fito daga gidansa, ya sa takunkumi, ya sa facemask, mutane ba sa sawa, cewar Elrufa'i. "In ka tsayar da mutum ka ce ya bai sa ba. Sai ya fito da ita daga aljihu. (Ya ce) yana da ita".

Gwamnan ya ce takunkumin wata kariya ce daga kamuwa daga ƙwayar cutar korona, kuma yana hana yaɗa cutar ga wasu mutane, idan mutum na ɗauke da ita.

An kuma tambayi Nasir Elrufa'i kan sane da halin da jama'arsa ke ciki musamman ma 'yan kasuwar jihar da ake ta raɗe-raɗin cewa sun fara bara, sai ya ce: "Sun fara bara?" Amma ai gwamma yin bara da mutuwa, in ji shi.

"Gara kai bara kana da rai, da ka mutu... Hakkin da Allah ya ɗora mana a jihar nan, (shi ne) mu kare lafiya da rayukan ɗan'adam. Kasuwanci za a iya tallafa musu," cewar Malam.

Idan komai ya koma daidai, za mu samu yadda za mu tallafa musu domin a koma harkokin kasuwanci kamar yadda aka saba a baya, gwamnan ya alƙawarta.


SOURCE:BBCHAUSA

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Coronavirus a Kaduna: Elrufa'i ya ce watakila zai sake rufe jihar"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?