LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Za a yi jarabawar NDA ranar 15 ga Agusta

Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Soji ta Najeriya (NDA) za ta yi jarabawar daukar sabbin kananan hafsoshi a ranar 15 ga watan Agusta, 2020.

Sanarwar da NDA ta fitar ranar Litinin ta ce za a fara rubuta jarabawar ne da misalin 7.00 na safe a dukkannin cibiyoyin jarabawar a fadin Najeriya.

Magatakardar NDA Birgediya Ayoola Aboaba, a cikin sanarwar ya ce ana bukatar “masu neman gurbin da su je da katin izinin rubuta jarabawar da takardar shaidar rajistar Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (UTME) da kananan hotuna guda biyu (masu girman inci 3.5 x 5)”.

Ya kuma bukaci kowannensu da ya rubuta cikakken suna da lambarsa ta jarabawar JAMB da jihar da ya fito da kwas din da ya zaba da cibiyar da ya rubuta jarabawar da kuma sa hannunsa a bayan kowane hoto.

“Kowane mai neman gurbi ya tabbata ya sanya takunkumi ko abun kare fuska domin ba za a bar marasa shi su shiga zauren rubuta jarabawar ba”, inji sanarwar.

SOURCE: https://aminiya.dailytrust.com.ng/

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments