--
Da duminsa: za'a bude makarantun sakandire a najeriya gobe talata 4/Agusta/2020

Da duminsa: za'a bude makarantun sakandire a najeriya gobe talata 4/Agusta/2020

A gobe Talata za a buɗe duk makarantun sakandire na gwamnatin tarayya 104 kamar yadda karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ya ba da sanarwa. Ministan ya ba da sanarwar hakan ne a ranar Litinin, 3 ga watan Agusta,

yayin da ya kammala tattaunawa da kwamishinonin ilimi na jihohi 36 da ke fadin tarayya da kuma sauran masu ruwa da tsaki. Cikin sanarwar da mai magana da yawun ma'aikatar ilimi ta tarayya, Ben Goong ya sanya wa hannu,

ya yabi shugabannin makarantun dangane da tabbatar duk wani shiri na komawar ɗalibai a gobe Talata. Tun a ranar 26 ga watan Maris ne Gwamnatin Tarayya ta rufe duk makarantun kasa, matakin da ya shafi makarantun gwamnati da na masu zaman kansu.

A farkon watan Yuli ne gwamnati ta ce ɗaliban sakandare 'ya ajin ƙarshe za su koma ajujuwansu amma ba lallai ne hakan ta tabbata ba kasancewar gwamnatin ta ce ba za a rubuta jarrabawar WAEC ba ta 2020.

Sai dai a yanzu gwamnatin ta ba da umarnin a buɗe makarantu a gobe Talata domin 'yan ajin karshe na makarantun sakandire su kammala shirinsu na zana jarrabawar WAEC wadda za a fara gudanarwa a ranar 17 ga watan Agusta.

A yayin da karamin ministan ilimin ke sanar da ranar buɗe makarantun, ya kuma bayyana karara cewa sai an kiyaye ka'idodin dakile yaduwar cutar korona yayin komawa. A cewarsa, dole ne kowace makaranta ta tanadi ruwan wanke hannu da kuma sunadarin tsaftace hannu (sanitizer).

Legit.ng ta ruwaito cewa, Jihohi Najeriya sun rarrabu dangane da damar da gwamnatin Tarayya ta bai wa ɗaliban ajin karshe ta komawa makarantu domin karasa shirin zana jarrabawar kammala karatun sakandire.

Binciken da jaridar The Punch ta gudanar ya nuna cewa, ɗaliban aji shida a jihohin Legas, Benuwe, Kwara da Ogun, na shirye-shiryen komawa a ranar Talata yayin da na jihar Cross River sun koma a yau Litinin. Har yanzu jihar Enugu, Gombe, da Ribas basu sanar da ranar komawar ɗalibansu ba, sabanin jihar Ekiti inda ɗaliban za su koma a ranar 10 ga watan Agusta.

Haka kuma, gwamnatocin jihohi da dama sun gaza tanadar wuraren wanke hannaye a karkashin ruwa mai gudana da kuma sunadarin tsaftace hannu kamar yadda kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona ya shata.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Da duminsa: za'a bude makarantun sakandire a najeriya gobe talata 4/Agusta/2020"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?