LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Boko Haram: Sojojin Najeriya sun mayar wa Gwamna Zulum martaniHukumomin sojin Najeriya sun ce za su yi bincike kan harin da ƙungiyar Boko Haram ta kai wa tawagar Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ranar Laraba da ta gabata, abin da gwamnan ya kira "zagon ƙasa" daga sojojin Najeriya.

Mai magana da yawun rundunar sojojin ƙasan Najeriya, Sagir Musa ya fitar da wata sanarwa, wadda a ciki ya ce ita ma rundunar ba ta ji dadin abin da ya faru ba kuma za ta gudanar da bincike a kan lamarin.

Sai dai rundunar ba ta taɓo zargin zagon ƙasa da Zulum ya yi mata ba.

A gefe guda kuma, masana kan harkar tsaro ne ke cewa akwai ƙanshin gaskiya a zargin da gwamnan ya yi cewa akwai zagon ƙasa daga ɓangaren sojoji.

"Zulum dai shi ne gwamna kuma ya fi kowa sanin matalar tsaro a jiharsa, saboda haka idan ya yi irin wannan zargi to abu ne da ya kamata a yi matuƙar dubawa," in ji Bulama Bukarti, wani bincike kan harkokin tsaro a Afirka.

Ya ƙara da cewa: Ni ina ganin akwai ƙanshin gaskiya a ciki domin kuwa ba shi ya fara yin zargin ba. Murtala Nyako, tsohon gwamnan Adamawa ya taɓa yin irin wannan zargi a Madagali."

"Mun san cewa sojoji sun cusa kansu cikin harkokin kamawa da cinikin kifi, sun shiga harkar noma kuma akwai zarge-zargen cin hanci da rasahawa. Saboda haka daidai ne idan aka ce an yi zagon ƙasa."

Wannan na zuwa ne yayin da jihar Borno ke ganin ƙaruwar hare-haren 'yan ta-da-ƙayar-baya, kuma ko a ranar Asabar sai da wani hari ya kashe mutum 15 ciki har da ƙananan yara a yankin kan iyaka cikin ƙasar Kamaru.

Gwamnan dai ya ce akwai buƙatar shugaba Muhammadu Buhari ya san cewa zagon ƙasan da ake yi daga cikin harkar tafi da tsaro na kawo cikas ga ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin 'yan ta-da-ƙayar-bayan na sama da shekara goma.

SOURCE:BBCHAUSA

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments