LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Da duminsa: INEC ta bude shafin yanar gizo da za a iya kallon sakamakon zabe kai tsaye

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kaddamar da wani shafin yanar gizo wanda jama'a zasu rinka duba sakamakon zabe kai tsaye.

A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, mai magana da yawun INEC, Festus Okoye, ya ce shafin zai "karfafa gudanar da sahihin zabe wanda babu magudi a cikinsa."

Ya ce amfani da shafin zai fara ne daga zaben maye gurbi na dan majalisar Nasarawa ta tsakiya wanda kuma za ayi amfani da shi a zaben gwamnonin Edo da Ondo.

Sai dai, Okoye ya ce shafin bashi da alhakin tattara sakamakon zabe, don haka, za a ci gaba da tattara sakamakon zabe kamar yadda aka saba. Tattara sakamakon zabe a zabukan da suka gabata ya zama babbar damuwa ga tsarin gudanar zaben Nigeria,

wanda a karshe ke sa jam'iyyu suki amince da sakamakon zaben. Ya ce INEC ta himmatu wajen magance duk wasu matsaloli da suka shafi demokaradiyyar zaben kasar, "lallai ya zama wajibi a kidaya kowacce kuri'a."

"Domin bunkasa sahihancin zabenmu, hukumar ta yanke shawarar samar da shafi a yanar gizo, mai taken "SAKAMAKON ZABEN INEC KAI TSAYE (IReV). "Shafin zai taimakawa 'yan Nigeria su rinka kallon adadin kuri'un da aka jefa a kowacce rumfar zabe a yayin da aka kidaya sakamakon zaben ranar," a cewar sanarwar.

"Hukumar na son sanar da jama'a cewa shafin ba shi da alhakin tattara sakamakon zabe. Za a ci gaba da tattara sakamakon zaben kamar yadda doka ta tanadar. "Za a ci gaba da cike takardu da kaisu cibiyar tattara sakamakon zaben har zuwa lokacin bayyana sakamakon.

"Hukumar na fatan cewa wannan ci gaba zai sa a rinka gudanar da sahihin zabe, kuma hankulan al'umma ya kwanta, tunda suna kallon duk kuri'ar da za a kirga a rumfar zabe kai tsaye." A yayin da hukumar ke shirin gudanar da zaben maye gurbi na Nasarawa a ranar Asabar, hukumar ta ce a karshen zaben, mutane zasu iya duba sakamakon zaben a shafinta na IReV.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments