--
Boko Haram: Zulum ya ce jami'an tsaro na yin zagon ƙasa a yunƙurin kawar da ƙungiyar

Boko Haram: Zulum ya ce jami'an tsaro na yin zagon ƙasa a yunƙurin kawar da ƙungiyar


Gwamnan jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya ya sake nanata cewa ƙoƙarin murƙushe ƙungiyar Boko Haram na shan zagon ƙasa daga wani rukuni na jami'an tsaron ƙasar.

Babagana Umara Zulum ya ce ba zai iya yin shiru cikin yanayi na kashe-kashe ba, saboda rantsuwar da ya yi tsakaninsa da Allah a kan zai kare al'ummar jiharsa.

Wannan na zuwa ne yayin da jihar Borno ke ganin ƙaruwar hare-haren 'yan ta-da-ƙayar-baya, kuma ko a ranar Asabar sai da wani hari ya kashe mutum 15 ciki har da ƙananan yara a yankin kan iyaka cikin ƙasar Kamaru.

Gwamnan dai ya ce akwai buƙatar shugaba Muhammadu Buhari ya san cewa zagon ƙasan da ake yi daga cikin harkar tafi da tsaro na kawo cikas ga ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin 'yan ta-da-ƙayar-bayan na sama da shekara goma.

Babagana Zulum na jawabi ne gatse-gatse kwanaki ƙalilan bayan kwambar motocinsa mai matuƙar tsaro kwatsam ta yanke tafiya, kuma ya juya ya tsere daga garin Baga na kusa da Tafkin Chadi saboda ɓarin wutar bindigogi babu ƙaƙƙautawa.

Sojoji sun ɗora alhakin abin da ya faru kan Boko Haram. Sai dai Zulum ya nuna cewa da hannunsu cikin abin da ya faru har ya sake amfani da kalmar "zagon ƙasa".

Wata sanarwa da aka wallafa a shafukan sada zumuntar gwamnan ta ambato shi yana faɗa wa takwarorinsa gwamnonin APC yayin wata ziyarar jaje ranar Lahadi cewa: "Zan ci gaba da yin tsayuwar daka, daram kan ƙudurin cewa Allah ne kaɗai ke ba da mulki.

Ba na neman wa'adi na biyu, idan ya nufe ni da kammala wannan ma, to na gode Allah. Amma ni a matsayina na gwamna, na yi shiru al'umma jihar Borno miliyan shida su mutu, su ƙare, hakan ba zai zama alheri gare ni ba.

Na yi rantsuwa tsakanina da Allah zan kasance mai gaskiya ga al'ummata," in ji Gwamna Zulum

Ya kuma tuhumi abin da ya sa sojojin Najeriya suka hana dubban mutanen da rikicin ya raba da gidajensu koma wa gonakinsu a lokacin da su sojoji ke noma a filaye.

BBC ta tuntuɓi rundunar sojin Najeriya don jin martaninta game da waɗannan manyan zarge-zarge, amma ta ce ba ta sa-in-sa da shugabannin siyasa.

Sai dai cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis jim kaɗan da aukuwar harin, rundunar sojin ta ce tana gudanar da bincike tare da yin taza da tsifa cikin yankin da lamarin ya faru a ƙoƙarinta na bin sawu da kuma sanya ƙafar wando ɗaya da maharan.

Haka zalika ta kuma ce ana gudanar da wani binciken don gano abubuwan da suka kai ga aukuwar hari.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, abin da ya faru, wani keɓaɓɓen al'amari ne a yankin da al'amura suka koma daidai, yayin da harkokin tattalin arziƙi ke ci gaba da kankama.

Rundunar sojin Nijeriya dai ta sake nanata tabbacinta ga jama'ar ƙasar cewa za ta bi diddigin abin da ya faru don hana sake aukuwarsa gaba.

Ta ma buƙaci al'ummar garin Baga da ma na ɗaukacin jihar Borno su ci gaba da bayar da sahihan bayanan da za su taimaka wa hukumomin tsaro wajen kamawa da bankaɗo asirin waɗanda suka kai hari.

'A bar mutane su koma gonakinsu'

Sai dai Zulum ya dage a kan matsayin cewa: "Akwai zagon ƙasa cikin harkar nan wadda ba za ta bari a kawo ƙarshen rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya ba. Shugaban ƙasa ya kwan da sanin wannan muhimmin batu.

Bugu da ƙari, ya kuma bayyana damuwa game da yawan mutanen da rikici ya raba da muhallansu a Borno, ya nunar cewa akwai buƙatar mutane su koma wuraren da aka samu wani yanayi na zaman lafiya.

"Muna da ɗumbin al'ummar da ba ta da hanyar zuwa gonakin noma, kuma talauci na ɗaya daga cikin tushen abubuwan da suka haddasa rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya.

Abin da muke buƙata shi ne inda aka samu zaman lafiya, a bar mutane su koma gidajensu. Ta yadda za su iya neman abin rayuwa," in ji Zulum.

Ya kuma ce: "Na faɗa sau da yawa cewa ba shakka ba za a iya kwatanta tsananin rikicin ta-da-ƙayar- bayan nan da abubuwan da suka faru a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015 ba, da kuma daga 2015 zuwa yanzu.

Shugaban ƙasa ya yi ƙoƙari, amma muhimmin abu shi ne, yana da kyau mu faɗi abin da ya dace".

Ba dai Gwamna Zulum ne, mutum na farko da ya bayyana cewa almundahana a cikin rundunar sojin ƙasar na tsawaita wahalar da mutane ke ciki a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

SOURCE:BBCHAUSA

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Boko Haram: Zulum ya ce jami'an tsaro na yin zagon ƙasa a yunƙurin kawar da ƙungiyar"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?