LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Masu Shoprite za subar Najeriya - Duba Dalili Anan

Shoprite za su yi gwanjon kaya, su na shirin barin kasuwanci a Najeriya Kamfanin kasar Afrika ta Kudun ya shafe shekaru akalla 15 a kasar nan


Bisa dukkan alamu dai kamfanin ba ya cin ribar kasuwancin da ya ke yi

Shararren kamfanin nan na Shoprite masu katafaren shaguna a kasashen Afrika har da Najeriya, sun bada sanarwar cewa za su fice daga kasar nan.

Rahotanni sun ce bayan shekaru 15 su na kasuwanci a Najeriya, Shoprite za su bar Najeriya. Kamfanin zai yi gwanjon kayan da ya rage masa ya bar kasar.

Shoprite ya bada wannan sanarwa ne a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, 2020. Hakan na zuwa ne bayan kamfanin ya fitar da bayanin yadda kasuwancinsa ya ke tafiya.

Rahoton kasuwancin Shoprite da ya fito karshen watan Yuni ya nuna cewa kamfanin kasar wajen ya na fuskantar kalubale wajen aiki a kasar Najeriya.

Kafin Shoprite, kamfanin Mr. Price da Woolworths sun bar Najeriya a baya. Duk wadannan kamfanonin kasar Afrika ta kudu ne da ake ji da su a Nahiyar nan.

A jawabin da kamfanin ya fitar, ya ce sakamakon ribar kasuwancinsu ya nuna zamansu ya kare a Najeriya, hakan na nufin asarar da Shoprite ya ke yi, ya yi kamari.

Cinikin da kamfanin ya ke yi ya yi kasa da 1.4% daga shekarar 2018 zuwa yanzu. Karancin cinikin kamfanin ya karu sosai a lokacin da aka hana fita saboda COVID-19.

A dalilin takunkumin COVID-19, sai da cinikin Shoprite ya yi kasa da 7.4%, ko da dai masu yi wa kamfanin ciniki su kan cika kwandonsu a wannan lokaci.

Wannan lamari zai iya sa dinbin mutane da su ke aiki da kamfanin su rasa sana’arsu. Watakila kuma barin Shoprite ya taimakawa wasu kamfanonin cikan gida.SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments