LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Wata Budurwa ta kashe saurayinta har lahira ta hanyar daba masa wuka A kirji

Wata Budurwa ta kashe saurayinta har lahira ta hanyar daba masa wuka

An zargi wata Budurwa da kashe saurayinta har lahira ta hanyar daba masa wuka a jihar legas.
Lamarin dai ya faru ne a Sagbokoji da ke yankin Apapa na jihar Legas, a karshen makon nan.
Wacce ake zargi mai kimanin shekaru 24 mai suna Nkechi, yanzu haka tana tsare a hannun ‘yan sanda.

Jaridar vanguard ta rawaito cewa budurwar wacce a ka fi sani da Omalicha tana zaune a gidan saurayin nata tsawan shekara daya, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.
Tun da fari Budurwar da saurayin nata mai suna Sulaiman mai shekaru 26 sun samu matsala, inda budurwar ke zargin sa da yaudarar ta.

A cewar wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, a dai dai lokacin da suke gudanar da shagul-gulan sallah da yammacin ranar Asabar sunji ihun neman taimako daga gidan da saurayin yake.
Da isar su, suka iske saurayin kwace cikin jini, inda yake kiran sunan budurwar sa da cewa ita ce ta caka masa wuka a kirji.'


Bayan Budurwar ta aikata hakan sai tai kokarin arcewa ta hanyar kokarin hawa jirgin ruwa da zai tsallakar da ita zuwa wajan da zata samu mafaka.

Sai dai hakan bai yu ba, inda tuni mazaunan yankin sukai ram da ita tare da damkata a hannun hukuma.

SOURCE: HUTUDOLE.COM

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments