LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Bidiyo da Hotuna: Ƴar Indimi ta auri biloniyan ɗan sarki, Malik Ado-Ibrahim

Adama Indimi, diyar hamshakin attajirin dan kasuwa, Muhammad Indimi na za ta auri biloniyan ɗan sarki, Malik Ado Ibrahim, wanda ya kafa kamfanin Bicernergy. Malik ne yarima mai jiran gado a masarautar Ohinoyi na yankin Ebira a jihar Kogi ta Najeriya.


An fara bukukuwan daurin aurensu ne a daren ranar Juma'a 7 ga watan Agusta a Maiduguri da saka lalle. Za a daura auren a yau Asabar 8 ga watan Agustan shekarar 2020 misalin karfe 10 na safe. Adama da Yarima Malik sun fara soyayya ne kimanin shekara guda da ya gabata kafin suka yanke shawarar za suyi aure.

A baya, Adama ta taba yin soyaya da shahararren mawakin Najeriya, Dbanji kamar yadda Linda Ikeji Blog ya ruwaito. Ga dai kayatattun hotunan yadda aka yi sa lallen a daren ranar Juma'a a Borno.

SOURCE: LEGIT

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN
FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments