--
’Yan sanda sun watsa masu zanga-zanga a Kaduna

’Yan sanda sun watsa masu zanga-zanga a Kaduna

’Yan sanda a Jihar Kaduna sun watsa taron masu zanga-zangar nuna alhinin kashe-kashe da ake yi a Kudancin Jihar.

’Yan sandan dauke da makamai sun tayar da taron ne a safiyar Asabar kafin wanda suka shirya shi su gama taruwa a mahadar Refinery Junction.

Kakakin ’yan sandan jihar, Mohammed Jagile ya ce, “Ba a sanar da mu ba. Mun je mun watsa taron na yau (Asaba) saboda haramtacce ne kuma yanzu kumai ya lafa.

Ba a samu wata arangama tsakanin bangarorin ba duk da cewa da farko ’yan sandan sun kama wasu masu zanga-zangar amma daga baya suka sake su.

Masu zanga-zangar sun fito ne sanye da bakaken kaya da ke alamta juyayin halin tashin hankalin da ake ciki a Kudacin.

Limis Alpha, daga cikin jagororin zanga-zangar ya ce zanga-zangar lumana ce domin bayyana damuwar jama’ar Kudancin Kaduna.

“An hana mu gudanar da zanga-zangar domin tun kafin mu taru motoci 15 zuwa 20 na ’yan sanda dauke da makamai sun isa wurin.

“Bukatarmu ita ce a samu kwanciyar hankali a kasa. Mun gode Allah komai ya tafi lafiya domin mu da ’yan sandan mun fahimci juna”, inji shi.

Ya ce sun tsara yin zanga-zangar ne ta hanyar daga kwalaye masu dauke da sakonni ba tare da yin jawabai ba, domin shuru ma magana ce.

Kudancin Kaduna ya dade yana fama da tashin-tashina musamman hare-haren kabilanci da daukar fansa da ya yi ajalin mutane da dama.

SOURCE: https://aminiya.dailytrust.com.ng/

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "’Yan sanda sun watsa masu zanga-zanga a Kaduna"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?