LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Bayan sallah za’a yi wa kudin tsarin mulkin kasar nan gyaran fuskaMajalisar dattijai ta ce za’a yi wa kudin tsarin mulkin kasar nan garanbawul da zarar an dawo daga hutun sallah.

Tuni shiri yayi nisa na yin gyare-gyare a kundin tsarin mulkin kasar nan, da za a ci gaba da gudanarwa jim kadan bayan kammala hutun Sallar Layya.

Sanata Ovie Omo-Agege wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar dattajai ne ya bayyana hakan, yayin da ya karbi bakuncin wasu kungiyoyin ci gaban mata da wanzuwar ilmi a birnin tarayya Abuja.

Majalisar dattijai ta ce za’a yi wa kudin tsarin mulkin kasar nan garanbawul da zarar an dawo daga hutun sallah.

Tuni shiri yayi nisa na yin gyare-gyare a kundin tsarin mulkin kasar nan, da za a ci gaba da gudanarwa jim kadan bayan kammala hutun Sallar Layya.

Sanata Ovie Omo-Agege wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar dattajai ne ya bayyana hakan, yayin da ya karbi bakuncin wasu kungiyoyin ci gaban mata da wanzuwar ilmi a birnin tarayya Abuja.Ya ce kwamitin da za su gudanar da aikin za su fara ka’in da na’in bayan hutun Sallar layya da za a yi a makon nan.

Sanatan ya jaddada cewa, shakka babu yayin gyaran kundin tsarin mulkin kasar, za a sanya dokoki da za su baiwa mata da yara kariyar da ta kamace su a Najeriya.

Ovie Omo-Agege ya kuma kara da cewa, duba da goyon bayan da suka samu daga fadar shugaban kasa, yana da cikakken kwarin gwiwa cewar kudurin zai samu kulawar da ta dace daga sauran bangarori masu ruwa da tsaki


SOURCE: FREEDOM RADIO KANO

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


Post a comment

0 Comments