--
'Yan bindiga sun kashe basarake a jihar Nasarawa

'Yan bindiga sun kashe basarake a jihar Nasarawa



Wasu 'yan bindiga da ba san ko su waye ba a daren ranar Juma'a sun kai hari garin Odu inda suka tayar da hankulan mutane suka kuma harbe dagajin Odu, Mr Amos Ewa Obere (ASP Rtd) har lahira.

Daily Trust ta ruwaito cewa Odu na karkashin garin Udege ne a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Nasarawa. An garzaya da basaraken da suka harba a cikinsa zuwa babban asibitin Udege domin yi masa magani amma ya mutu a asibitin.

Kafin rasuwarsa, marigayi Obere wanda tsohon jami'in dan sanda ne mai mukamin mataimakin sufeta shine dagajin garinsa da kauyukan da ke kewaye. Shaidun ganin ido sun shaidawa majiyar Legit.ng cewa 'yan bindiga masu yawa ne suka isa garin suna harbe harbe wanda hakan ya firgita mutane sannan suka tafi suka aikata mummunan abinda ya kawo su.

"Da suke dira garin, sun kama hanya zuwa fadar basaraken suka fito da shi suka fada masa cewa kwanakin ka sun kare a duniya. "Sannan suka harbe shi da bindiga. "Sun tsere kafin mutane su isa fadar su san abinda ke faruwa," in ji shi. Shugaban kungiyar 'yan jarida, NUJ, na farko a jihar Nasarawa,

Mr Joel Oga wanda shima dan asalin garin ne ya tabbatar da afkuwar lamarin da ya ce abin bakin ciki ne. Ya kuma bayyana halin rashin tsaro a karamar hukumar ta Nasarawa a matsayin abin tsoro, inda ya ce, "Na yi shekaru biyu ban tafi garin mu ba saboda rashin tsaro." Yunkurin da aka yi na ji ta bakin shugaban karamar hukumar Nasarawa, Mohammed Otto da Kakakin Rundunar 'Yan sandan jihar, Rahman Nansel ya ci tura domin wayoyinsu a kashe su ke.


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "'Yan bindiga sun kashe basarake a jihar Nasarawa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?