LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

An kama wani matashi bayan ya saci dan kamfai na mata da aka yi amfani da su har guda 14

Wani matashi mai suna Adeniyi Muhammed ya shiga hannun 'yan sanda a kan satar dan kamfai na mata da aka yi amfani dasu guda 14 a jihar Ogun 

An kama wanda ake zargin ne bayan wata mazauniyar unguwar Kano a yankin Ayetoro da ke jihar ya shigar da kara a kan satar dan kamfenta a ranar Talata, 18 ga watan Agusta 

Sai dai ya ce wani ne ya aike shi sato dan kamfen, kuma ana kokarin ganin an kamo shi An kama wani matashi mai suna Adeniyi Muhammed dan shekaru 16 dauke da dan kamfai na mata da aka yi amfani dasu guda 14 a jihar Ogun, shafin Linda Ikeji ya ruwaito. 

Kakakin ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan wata mazauniyar unguwar Kano a yankin Ayetoro da ke jihar ta shigar da kara a kan satar dan kamfenta a ranar Talata, 18 ga watan Agusta. 

Oyeyemi ya ce: “An gudanar da bincike a gidan da yake zaune sannan aka samo wasu karin ‘yan kamfai 14. Wanda ake zargin ya tona cewar ya aikata laifin amma ya yi ikirarin cewa wani ne ya tura shi domin ya samo masa ‘yan kamfen. Ana kokarin ganin an kamo abokin aikin nasa.” 

An kuma tattaro cewa kwamishinan yan sandan jihar, Edward Ajogun ya yi umurnin cewa a tura wanda ake zargin zuwa sashin binciken laifuffuka na jihar domin ci gaba da bincike. 

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments