LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Uba ya yiwa diyarshi fyade don ya tabbatar da budurcinta

‘Yan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 40 da aka ambata da suna Gbenga Taiwo, bisa zargin lalata ‘yar cikinsa mai suna Folake. Taiwo wanda ya kasance bazawari na zama tare da ‘yarsa mai shekaru 15 a wani gida da suke haya a Baruwa, yankin Ipaja da ke jihar Lagas. 

Jaridar Punch ta ruwaito cewa mahaifin yarinyar na yawan cin zarafinta ta hanyar tura yatsa a matancinta tun tana ‘yar shekara 13 a duniya. Sakamakon gajiya da cin zarafin da yake mata, sai Folake ta yi karar mahaifin nata a gaban mai gidan da suke haya inda shi kuma ya gargadi Taiwo da ya janye daga ta’asar da yake yi. 

An tattaro cewa ya ci gaba da aikata hakan lamarin da ya sa yarinyar kai karansa wajen kawunta kwanaki. Yayinda kawun nata ke kokarin magance lamarin cikin sirri, sai wani makwabci ya bangado lamarin sannan ya yi kara. 

An tattaro cewa an kai karar lamarin ga offishin ‘yan sandan Ipaja sannan aka kama Taiwo a ranar Asabar da ya gabata. Jagoran kungiyar kare hakkin yara da ke bibiyar lamarin, Mista Ebenezer Omejalile, ya fada ma City Round cewa Taiwo ya yi ikirarin cewa yana zargin Folake na bin maza don haka ya yanke shawarar binciken budurcinta da yatsarsa. 

Ya ce: “Mahaifin yarinyar ya sha cin zarafinta tun tana shekara 13. Ya kai kimanin shekaru 40 a duniya kuma ya kasance mai aikin gyaran wuta da ya yi ritaya. “Kafin kawun yarinyar ya shiga lamarin, wani Mista Alagba, yarinyar ta gaji da muguntan da mahaifinta ke yi mata sannan ta sanar da mai gidan da suke haya wanda ya tunkari mahaifin nata a kan ya daina mugun aikin da yake yi sannan ya sanar dashi illar abunda yake yi.

“Amma sai ya yi kunnen uwar shegu sannan ya ci gaba da lamarinsa hart a kai duk lokacin da yake aikin dare, sai ya tafi da yarinyar domin ya ci gaba da lalata da ita har sai ya gamsu. “Mutumin ya yi ikirarin cewa ya ga wasu hotuna a wayar ‘yar tasa sannan yana zargin tana bin maza. Ya ce bai tara da ita ba kawai dai ya yi amfani da hannunsa ne wajen duba ko budurwace ko akasin haka.”


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657 

Post a comment

0 Comments