LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

An kama basarake yana lalata da diyarshi, ya suma a ofishin yansanda bisa wani dalili

Yan sandan jihar Ogun sun damke wani basaaraken gargakiya mai suna Rasheed Sholabi sakamakon yi wa diyar cikinsa mai shekara 15 fyade.

Kakakin yansandan jihar Ogun Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa manema labari haka ranar 6 ga watan Agusta.

Ya ce diyarsa mai suna Abimbola ce ta shigar da kara a caji ofis na yansanda da ke Owode Egbado, sakamakon haka yan sanda suka tafi da shi domin amsa tambayoyi.

Abimbola ta shaida wa yansanda cewa mahaifinta ya yi ta yi mata fyade tun tana da shekara 11, ta ce sakamakon yadda mahifinta ke lalata da ita ya haifar mata da matsala, kuma yanzu haka bata iya rike fitsari.

Da farko basaraken ya jajurce wajen musanta zargin, amma sai ya suma bayan wata tsohuwar matarsa ta shida wa yansanda cewa ta kashe aure tare da shi ne saboda ta taba kama shi turmi tabarya yana lalata da diyarshi Abimbola wacce mahaifiyarta ta rasu tun tana yar shekara 2 a Duniya.

Yansanda na ci gaba da bincike kan lamarin.

SOURCE: ISYAKU.COM

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments