LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Allah ya tona asirin makauniyar karya mai bara bayan an gano cewa idanunta garau suke

Allah ya tona asirin wata makauniyar karya yau a birnin Abakaliki na jihar Ebonyi bayan ta tabbata cewa lafiyar idanunta kalau.

Asirin matar ya tonu ne bayan ta shafa Robb a idanunta kuma ta fara hawaye, sai ta umarci yaro da ke tare da ita ya jagorance ta domin ta karbi sadaka daga wajen mutane a mahadar Union Bank da ke Abakaliki.

Bayanai sun nuna cewa matar yar asalin jihar Imo ce.

Wani hadimin Gwamnan jihar Ebonyi ne ya kamata, bayan na'urar tsaro ya nada abin da take yi. Sakamakon haka ya kalubalance ta, bayan an buda idanunta sai aka gano cewa lafiyarta kalau, haka zalika ba abin da ya sami idanunta.


SOURCE: ISYAKU.COM

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments