--
Yanzu-yanzu: WAEC ta sanar da ranar fara jarrabawa

Yanzu-yanzu: WAEC ta sanar da ranar fara jarrabawa



Hukumar jarrabawa ta WAEC ta sanar da ranar fara jarrabawar masu kammala sakandire na shekarar 2020 Za a yi jarabawar tsakanin 4 ga watan Augusta zuwa 5 Satumban 2020

Karamin ministan ilimi, Emeka Nwajuiba ne ya sanar da hakan a yayin taron kwamitin yaki da cutar korona ta kasa Hukumar jarrabawa ta yammacin Afrika (WAEC) ta sanar da ranar fara jarrabawar masu kammala sakandire na wannan shekarar.

Wannan sanarwar ta zo ne a yayin bayanin da kwamitin yaki da cutar korona ta fadar shugaban kasa (PTF) karkashin shugabancin Boss Mustapha, ke yi a Abuja.

Kwamitin yaki da cutar korona ta kasa ya tabbatar da cewa za a yi jarabawar tsakanin 4 ga watan Augusta zuwa 5 Satumban 2020. Karamin ministan ilimi, Emeka Nwajuiba ne ya sanar da hakan a yayin taron.

Kamar yadda hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Twitter: "Gwamnantin tarayya ta sanar da cewa za a fara jarabawar WAEC daga ranar 4 ga watan Augusta zuwa 5 ga watan Satumba.

"Karamin ministan ilimi ne ya sanar da hakan a jawabin kullum na kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da korona a Abuja." A gefe guda, mun ji a baya cewa gwamnatin jihar Kano ta yi magana dangane da jita-jitar da ke yaduwa a tsakanin al'umma na cewa a yau Litinin, 6 ga watan Yuli, za a bude makarantu ga wani rukuni na dalibai.

Legit.ng ta rawaito cewa, wasu daga cikin rukunin daliban da gwamnatin tarayya ta ba da umarnin a bude musu makarantu, sun shirya abinsu sun tafi makarantu da safiyar yau ta Litinin. Sai dai fa sun riski makarantun a rufe, lamarin da ya sa a dole suka dawo gida ba bu shiri kuma ba tare da sun yi farin ciki a kan lamarin ba.

A yayin da 'yan kwanakin nan al'umma jihar Kano suka yi ta rade-radin za a bude makarantu a yau Litinin, wani gargadi da gwamnatin jihar ta yi ya disasashe duk wani tsammaninsu.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu-yanzu: WAEC ta sanar da ranar fara jarrabawa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?