--
Yanzu-yanzu: DSS ta cafke Magu, shugaban EFCC

Yanzu-yanzu: DSS ta cafke Magu, shugaban EFCC



Hukumar 'yan sandan fararen kaya (DSS) ta kama Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa tare da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).

An damkesa ne bayan kwanaki kadan da Abubakar Malami, antoni janar kuma ministan shari'ar Najeriya ya zargesa da almundahana. Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, shugaban EFCC ya yi tafiya zuwa birnin Dubai da ke daular larabawa ba tare da sanin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba kuma a yayin kullen kasa.

A lokacin da aka tuhumesa, ya ce ya je wani bincike ne. Ana zargin shugaban da rayuwar da ta fi abinda yake samu daga aikinsa. Karin bayani na nan tafe... SOURCE: LEGIT.NG



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu-yanzu: DSS ta cafke Magu, shugaban EFCC "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?