--
Yanzu Yanzu: An hana mataimakin gwamnan Oyo shiga wajen addu’an takwas na Ajimobi

Yanzu Yanzu: An hana mataimakin gwamnan Oyo shiga wajen addu’an takwas na Ajimobi

Yanzu Yanzu: An hana mataimakin gwamnan Oyo shiga wajen addu’an takwas na Ajimobi Hoto: The Nation Source: UGC


An hana mataimakin gwamnan jihar Rauf Olaniyan shiga wajen addu’an kwana takwas na rasuwar Ajimobi wanda aka gudanar a harabar gidansa - Iyalan mariayin sun sanar da cewar taron addu’an zai zama na takaitattun jama'a, inda suka bukaci jama’a da su kalla ta yanar gizo

Olaniyan ya jira na dan lokaci bayan an ce makullin na wajen matar marigayin, amma daga bisani ya wuce bayan kin bude masa An sha ‘yar dirama a ranar Lahadi a Oluyole, gidan marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, lokacin da aka hana mataimakin gwamnan jihar Rauf Olaniyan shiga wajen addu’an kwana takwas na rasuwarsa,

wanda aka gudanar a harabar gidansa. Iyalan mariayin sun sanar da cewar taron addu’an zai zama na takaitattun jama'a, inda suka bukaci jama’a da su kalla ta yanar gizo kamar a Zoom, YouTube da Facebook.

Olaniyan ya isa gidan da misalin 11:20 na safe a ayarin motoci biyar. Amma da ya kofar da zai shigar dashi hanyar gidan Ajimobi, sai yan sanda da sauran jamián tsaro suka dakatar da ayarin motocin. Suka ce lallai sai dai motai mataimakin gwamnan nekadai za a bari ya shiga unguwar don halartan taron.

Da fari jami’an tsaron gwamnan sun ki amincewa da shawarar amma a lokacin da hayaniyarsu ya yi yawa, sai wani babban dan sanda ya sanya baki sannan suka amince cewa motar mataimakin gwamnan kadai ya shiga.

Amma da suka isa gidan Ajimobi, sai suka kara tarar da kofar a rufe. Hadiman mataimakin gwamnan sun gabatar da ubangidansu amma aka sanar masu da cewar an rufe kofar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Sannan cewa uwargidar Ajimobi ce ke rike da makullin. Olaniyan ya jira inda yake tunanin za a magance lamarin kan lokaci. Bayan ya jira tsawon mintuna 15 ba tare da wani ci gaba ba sai Olaniyan ya bar gidan.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu Yanzu: An hana mataimakin gwamnan Oyo shiga wajen addu’an takwas na Ajimobi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?