--
BINCIKE: Ko kun san me yasa mata ke jin ciwo yayin zuwan al’adarsu?

BINCIKE: Ko kun san me yasa mata ke jin ciwo yayin zuwan al’adarsu?



Mata da yawa duk lokacin da jinin al’ada zaizo da kwana biyar ko bayan kwana biyu da al’ada, za suji yanayin jikin su ya canja duk su rasa meke damun su wannan shi ake kira PRE-MENSTURAL SYNDROME (PMS)
Wannan PMS din wani lokacin yakan tarwatsa zamantakewar aure, zamantakewar soyayya, ko rashin jituwa da yan uwa ko iyaye, saboda rashin fahimtar wannan PMS din..
Mafiyawan matan dake da wannan matsalar suna kasancewa cikin matsanancin hushi, bacin rai, tunani maras dalili, rashin hakuri da saurin kuka akan abunda bai taka kara ya karya ba.. Kuma macce zata iya mayarwa mutum magana cikin hushi, musamman miji ko saurayi. Wani lokacin ma miji zaiyi tunanin ko matar shi bata son shi ne… BA HAKA BANE… MU FAHIMCE WANNAN.

✅ MEKE HADDASA WANNAN PMS din?
Har yanzu babu tabbataccen abunda ke kawo wannan matsalar, amma bincike ya tabbatar da rashin daidaituwa tsakanin hormones ne (oestrogen da progesterone da progestin)

✅ MENENE ALAMOMIN
daga kwana biyar kafin zuwan al’ada har kwana 3 bayan alada ko kasa da haka, macce zata fara jin wadansu daga cikin wadannan koma duka

➡️Damuwa sosai da rashin jin dadi
➡️Ciwon kai
➡️Kunburin da cikar nonuwa
➡️Hushi da zafin rai
➡️Fargaba
➡️Rudewa da rashin ajiye hankali idan ana mata magana
➡️Cin abinci sosai ko rashin cin abincin
➡️Kabewar ciki

✅ SUWA SUKAFI FAMA DA IRIN WANNAN MATSALAR?
Mafiyawan su mata ne yan shekara 18 zuwa shekara 25, amma idan macce tafara haihuwa, abun zai rage sosai koma ya daina…

MENENE MAGANI?
✅ Yakamata yan uwan macce da mijinta ko wanda zaya aure ta ya fahimce cewa, idan al’adar macce zatazo, takan zo mata da irin wadannan canje canjen, dan haka ayi hakuri da ita bada sonta take wadansu abubuwan ba..
✅ Abinci maigina jiki da kayan ganye da yayan itatuwa suna taimaka wa wajen daidaita MOOD
✅ Idan yayi tsanani, ana amfani da drugs kamar group din(SEROTONIN REUPTAKE INHIBITORS )
✅ Kada aci abinci da gishiri lokacin da abun yake tasowa, saboda gishiri na kara hawan jini a wannan lokacin
✅ Motsa jiki na taimakawa sosaiiii
✅ Aba macce dama tayi abunda ke saka ta nishadi, kamar kallo, rawa, karatun littafai da sauran su.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "BINCIKE: Ko kun san me yasa mata ke jin ciwo yayin zuwan al’adarsu?"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?