--
Buɗe makarantu: Gwamnatin Tarayya za ta gana da gwamnatocin jihohi a ranar Talata

Buɗe makarantu: Gwamnatin Tarayya za ta gana da gwamnatocin jihohi a ranar Talata

Kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona yayin ganawa da shugaba Buhari Source: Twitter


Gwamnatin Tarayya za ta gana da gwamnatocin jihohi ranar Talata don tattaunawa kan tsare-tsaren da za a bi wajen buɗe makarantun firamare da na sakandire domin 'yan ajin karshe. Tun a watan Maris ne gwamnati ta ba da umarnin rufe kafatanin makarantu a fadin tarayyar kasar biyo bayan bullar cutar korona wadda a yanzu da ta harbi sama da mutum 25,000.

A ranar Litinin ne shugaban kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona, Boss Mustapha, ya ba da sanarwar buɗe makarantu, domin ba wa 'yan ajujuwan karshe damar kammala shirinsu na zana jarrabawa.

Sai dai kungiyar kiwon lafiya NMA da kuma ta malamai NUT, sun ce wannan shawara da gwamnatin tarayya ta yanke ka iya jefa malamai da kuma dalibai cikin hatsarin kamuwa da cutar. Duk da wannan umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar na sake buɗe makarantu, har yanzu jihohi na ci gaba da gwagwarmayar yanke hukunci kan ranakun sake buɗe makarantun.

Akwai jihohi da dama da suka amince da umarnin gwamnatin tarayya na buɗe makarantun amma har kawo yanzu ba su cimma matsaya kan lokacin da za su aiwatar da hakan ba. Galibinsu ba su kammala shimfida tsare-tsaren da za su bi ba domin bai wa wan rukuni na dalibai damar komawa ajujuwansu domin su ci gaba da daukan darasi.

Daga cikin jihohin da ke shirye-shiryen buɗe makarantu sun hadar da; Edo, Katsina, Osun, Bauchi, Ogun, Enugu, Filato, Delta, Gombe, Neja, Taraba, Benuwe, Kwara, Ebonyi, Cross River, da kuma Ribas

Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Legas ta sanar da cewa za ta buɗe makarantu a ranar Litinin 3, ga watan Agusta. Kamar yadda gwamnatin tarayya ta ba da umarni, gwamnatin Legas ta ce daliban aji shida na firamare, da 'yan aji uku da kuma 'yan aji shida na makarantun sakandire, su kadai za su koma makarantu a wannan rana.

Gwamnatin jihar ta sanar da hakan ne cikin wani sako da ta wallafa kan shafinta na Twitter a ranar Asabar, 4 ga watan Yuli, lamarin da ta ce an bai wa daliban damar komawa domin su kammala shirin zana jarabawa.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Buɗe makarantu: Gwamnatin Tarayya za ta gana da gwamnatocin jihohi a ranar Talata "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?