--
Mijina yana kira na da Alade, a taimaka a tsinke igiyar aurenmu - Matar aure

Mijina yana kira na da Alade, a taimaka a tsinke igiyar aurenmu - Matar aure




Matar aure ta nemi wata kotun gargajiya da ke Mapo da ta tsinke aurensu mai shekaru 12 da mijinta -Ta bukaci sakin ne kan hujjar cewa mijin nata mai suna Segun na kwatanta ta da alade - Mai shari'a Ademola Odunade,

shugaban kotun tare da sauran alkalan biyu sun amsa bukatar matar tare da mallaka mata yaran da suka haifa da mijin nata Wata matar aure mai yara uku da aka ambata da suna Oluwayemisi Ajakaye a ranar laraba, ta bukaci wata kotun gargajiya da ke Mapo, jihar Ibadan da ta tsinke aurensu mai shekaru 12 da mijinta.

Matar ta nemi takardar sakin ne kan hujjar cewa mijin nata mai suna Segun na kwatanta ta da alade. Kamar yadda ta sanar da alkalin, ta ce: "Ya zargeni da bin maza duk da bana yi. A cikin shekarun nan, Segun baya barina cikin kwanciyar hankali. "Ya zargeni da lalata da 'yan uwana, makwabta, 'yan kasuwa da kuma fasto."

Ta zargi Segun da kiran mahaifiyarta a waya tare da barazanar kasheta a gabanta, jaridar Daily Trust ta ruwaito. Amma kuma, wanda ake karar bai halarci zaman kotun ba balle ya kare kansa a game da laifukan da ake zarginsa. Mai kare wanda ake karar ya ce an kai wa Segun takardar gayyata.

Mai shari'a Ademola Odunade, shugaban kotun tare da sauran alkalan biyu sun amsa bukatar matar. Odunade ya bukaceta da ta rike dukkan yaransu uku tare da umartar Segun da ya dinga biyan mahaifiyar yaransa N15,000 a kowanne wata na kula da su.

A gefe guda, wani kotu na musamman a Legas da ke sauraron karar fyade da rigimar iyali ya yankewa wani ‘dan acaba mai shekaru 37 daurin shekaru 20 a gidan kurkuku.

Jaridar Vanguard ta ce wannan kotu da ke zama a garin Ikeja ya samu Emmanuel Idoko da laifin keta alfarmar ‘diyar cikinsa mai shekara 12 da haihuwa. Alkali Sybil Nwaka yayin da ya ke zartar da hukunci ya ce masu kara sun gabatar da hujjojin da ke tabbatar da cewa Mista Emmanuel Idoko ya aikata wannan laifi.

SOURCE: LEGIT.NG

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Mijina yana kira na da Alade, a taimaka a tsinke igiyar aurenmu - Matar aure "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?