--
Duba yanda Mutane 244 sukayi yunƙurin yin aikin Hajji ta ɓarauniyar hanya

Duba yanda Mutane 244 sukayi yunƙurin yin aikin Hajji ta ɓarauniyar hanya




Jami'an tsaron da ke kula da aikin Hajji sun kama mutum 244 da suka yi yunƙurin shiga Masallacin Harami domin gudanar aikin Hajji ta ɓarauniyar hanya.

Tuni aka hukunta su a cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labaran Saudiyya (SPA) ya rawaito, wanda kuma jaridar Saudi Gazette ta wallafa.

Wani mai magana da yawun rundunar jami'an tsaron ya yi kira ga mazauna Saudiyya da su bi dokokin aikin Hajjin sau-da-ƙafa, waɗanda aka saka domin kare mutane daga kamuwa da cutar korona.

"Jami'an tsaro sun tsaurara tsaro a ciki da kewayen Masallatan Harami domin tabbatar da waɗannan dokoki tare da kama masu ƙetara su," in ji shi.

SOURCE: BBCHAUSA

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Duba yanda Mutane 244 sukayi yunƙurin yin aikin Hajji ta ɓarauniyar hanya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?