LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Duba Yadda wani mashi ya kashe wata budurwa yayin da suke tsakiyar lalataWani mutum dan kasar Burtaniya da ake zargi da fyade da kashe wata abokiyarsa ya shaidawa kotu cewa ta mutu ne sakamakon "tsautsayi da aka samu lokacin da suke saduwa". An bukaci mutumin, Wesley Streete, mai shekaru 20, ya raka yarinyar, Keeley Bunker zuwa gidanta ne bayan sun dawo daga club da daddare tare da wani abokinsu a birnin Birmingham.

A ranar 19 ga watan Satumban shekarar 2019 ne Bunker ya bayyana cewa ya jefa gawar ta a wani kududufi da ke kusa da su kuma ya rufe da rassan bishiya kamar yadda ya shaidawa kotu.

Kawun yarinyar ya gano gawar ta yayin da suke bincike a Wigginton Park da ke Tamworth, Staffordshire kimanin nisan kilomita 23 arewa maso gabashin Birmingham.

Da ya ke kare kansa a gaban kotu a karo na farko, Streete ya bayyana abinda ya yi ikirarin ya faru kafin mutuwar ta. Ya amince da cewa tabbas sun tafi club tare a birnin Birmingham tare da Bunker da wata Monique Riggon kafin daga baya suka koma gidansu da Tamworth. Su uku suka isa gidan Riggon amma Bunker ta ce tana son ta tafi gidan ta ta kwana a gadonta hakan yasa aka ce Streete ya yi mata rakiya.

Ya yi ikirarin cewa sun fara hirar masoya a hanya sannan suka sumbaci juna kana suka yi lalata a Wigginton Park. "Na shake mata wuya a lokacin da muke lalata kuma tsautsayi yasa ta mutu," in ji shi. Ya amsa cewa ya yi wa iyalanta da abokansa da yan sanda karya game da abinda ya faru saboda yana jin kunyar halin da ta mutu.

"Na firgita kuma ban san yadda zan fada wa mutane halin da ta mutu ba. Na ji tsoron fada wa yan sanda, sauran mutane, mahaifi na da mahaifiya na," in ji shi. Streete ya ce ya san Bunker ta hannun wani abokinsa da suka taso tare kuma ya fada wa kotu cewa su abokai ne. Ya ce sun sha giya da wiwi "misalin sau hudu a mako" daga karfe 5 na yamma zuwa 8 na dare a Wigginton Park. A daren da ta mutu,

ya ce yana tunanin akwai yiwuwar ya sha wiwi a lokacin da ya ke shan giya har kofi uku. Streete ya ce yana tunanin ya yi tatil da giya a lokacin da suka isa gidan Riggon amma dai yana iya tafiya duk da cewa yana cikin maye. Masu bincike sun shaidawa kotu cewa Streete ya sauya labarinsa a kalla sau hudu tun da aka fara shari'ar.

SOURCE: LEGIT.NG

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments