--
Kaduna: NSCDC sun cafke Faston da ake zargi da fyade da yin lalata a Barnawa

Kaduna: NSCDC sun cafke Faston da ake zargi da fyade da yin lalata a Barnawa

Fasto Joseph Alhassan na cocin Faith Agape Church a Narayi, jihar Kaduna, ya shiga hannun jami’an tsaro bisa zargin cewa ya dade ya na lalata da wata yarinya ‘yar shekara 16. Jami’an hukumar NSCDC na reshen jihar Kaduna sun damke Joseph Alhassan ne a gidansa da ke kan titin Abdulrahman a unguwar Barnawa da ke garin Kaduna.

Hukuma ta yi nasarar cafke wannan Bawan Allah bayan ma’aikatar kula da jama’a da walwalar al’umma a jihar Kaduna ta kai kararsa gaban jami'an tsaro a ranar Asabar. A yayin da wata jami’ar gwamnati, Brenda Bartholomew, ta yi hira da ‘yan jarida, ta ce wanda ake zargi watau Joseph Alhassan ya shafe shekaru biyar ya na tarawa da wannan yarinya.

Brenda Bartholomew ta ke cewa wannan Fasto ya yi ta amfani da yarinyar ne ba tare da amincewar ta ba. An yi wannan ne a lokacin da yarinyar ta ke aiki a matsayin boyi-boyinsa. Ainihin wannan yarinya, mutumiyar garin Saminaka ce, a karamar hukumar Lere, kuma tun ta na ‘yar shekara 11 ta ke zama da malamin addinin kamar yadda NAN ta rahoto.

Gwamnan Jihar Kaduna da Mataimakiyarsa Source: Twitter



Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta ce kungiyar Bridge that Gap Initiative ce ta fara kawo kukan wannan mutumi, wanda hakan ya jawo gwamnatin Kaduna ta binciki lamarin. “Bayan mun samu bayani, mun kai maganar gaban ofishin hukumar NSCDC da ke karamar hukumar Kaduna ta kudu, a Kakuri.”

Inji jami’ar ma’aikatar kula da jama’a da walwalar al’ummar. Misi Bartholomew ta cigaba da cewa: “Bayan nan ne dakarun NSCDC su ka kama Alhassan, kuma yanzu ana binciken lamarin.” Bisa dukkan alamu nan gaba kadan za a gurfanar da wannan malamin coci a gaban kotu domin amsa laifin da ke kansa.

“Mun kai ita (wanda ake zargin an yi amfani da ita) zuwa cibiyar kula da wadanda aka yi wa fyade a Kakuri, domin a duba lafiyarta, a yayin da mu ke jiran NSCDC su kammala bincikensu, kafin mu yi gaba, mu shigar da kara a kotu.”

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657



0 Response to "Kaduna: NSCDC sun cafke Faston da ake zargi da fyade da yin lalata a Barnawa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?