--
Tilas ne surukar Ganduje tayi takabar kwana 130 – Cewar Sheikh Muideen

Tilas ne surukar Ganduje tayi takabar kwana 130 – Cewar Sheikh Muideen



Wani rahoto ya bayyana cewa yayin da aka gabatar da addu’ar kwana 8 ta tsohon gwamnan Oyo Abiola Ajimobi a jiya a Ibadan, wani Malamin addinin Musulunci mai suna Sheikh Muideen Ajani Bello, ya ce matar marigayin Mrs Florence Ajimobi, dole tayi zaman takaba na kwanaki 130 kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Wannan dai ya zo ne bayan Malamin ya bayyana cewa duka wadanda suke ta yabon marigayin a yanzu da ya mutu Allah sai yayi musu hukunci.

Sheikh Bello ya bayyana hakane a lokacin addu’ar kwana takwas din wacce aka gudanar a gidan marigayin dake Oluyole.

Anyi kokarin bin ka’idoji da hukumomin lafiya suka sanya na COVID-19, inda iya mutane kalilan aka bari suka shiga wajen.

Malamin ya ce: “Duka wadanda suke yabon Ajimobi bayan ya mutu, kuma basu yi hakan ba a lokacin da yake raye, duka sai Allah ya hukunta su.

“Kowacce halitta za ta mutu. Ajimobi yayi abin alkhairi a lokacin da yake da rai. Ya gina Masallaci domin Allah.

“Rayuwa ba komai ba ce. A lokacin da muke binne shi na tambayi kai na, shin ba gawar wannan mutumin ba ce da yayi wannan ginin muke sanyawa a cikin kabari?”

Dangane da matar marigayin, ya ce dole sai tayi zaman takaba na kwanaki 130.

“Ke kuma matar mai girma, zaki yi zaman takaba na watanni 4 da kwana 10. Za ki gama zaman takaba a ranar 2 ga watan Nuwamba, 2020. A lokacin da kike zaman takaba, ki dinga yiwa mijinki addu’a.

“Bayan kin kammala zaman takabar, komai ya wuce. Ki kula da ‘ya’yanki. Ki koyar da ‘ya’yanki tarbiyyar da za a dinga yabon Ajimobi tamkar bai mutu ba.”

Wadanda suka halarci taron addu’ar sun hada da matar marigayin, Mrs Florence Ajimobi, Sanata Teslim Folarin, tsohon gwamnan jihar Oyo, Otuba Adebayo Alao Akala.

Haka kuma akwai, Alhaji Kunle Sani, babban Malamin addinin Musulunci, iyalan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Bahir Olanrewaju Eleshinmeta, Alhaji Sadudeen Adekilekun.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Tilas ne surukar Ganduje tayi takabar kwana 130 – Cewar Sheikh Muideen"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?