--
Duba Bishiya mai shekaru 300 da ake zargin tana komawa mutum tsakar dare

Duba Bishiya mai shekaru 300 da ake zargin tana komawa mutum tsakar dare



Wata bishiya a kasar Ghana mai suna Mpeni Kofi ana zargin tana komawa mutum don bai wa jama'a kariya  An gano cewa bishiyar ta kai shekaru 300 a duniya kuma ita ce ke gadin jama'ar Akuapem a cikin dare

Abinciken da jaridar Legit.ng tayi ta duba tsohon tarihin bishiyar mai cike da al'ajabi da bada mamaki wacce take tun zamanin kaka da kakanni Wata bishiya mai suna Mpeni Kofi a kasar Ghana mai shekaru 300 a duniya,

ana zargin tana komawa dogon mutum dan Adam don bai wa jama'ar yankin kariya. Har a yanzu saiwoyin bishiyar na nan kuma ganyayyakinta koraye duk da karni 30 da ta kwashe a duniya. Wasu jama'ar yankin na bautar bishiyar kamar yadda kaka da kakanninsu ke yi. Jama'ar Akuapem na zargin cewa bishiyar ce ke basu kariya, Ghanaweb ta ruwaito.

Legit.ng ta gano cewa mukaddashin shugaban Akuapem, Nana Addo Kwataa da mataimakinsa, Ahenenanhene Osae Adade, sun bayyana cewa bishiyar na da wasu alamu na mutuntaka. Bishiyar da aka rufe da farin launi ta kasan ta, magabatansu na cewa ta taba karesu daga harin yaki da aka kai musu.

A yayin tuna tarihin jama'ar Akuapem, Nana Addo Kwataa ya ce suna ganin Mpeni Kofi a matsayin wani abu na musamman da ke shiryar da su. Kamar yadda yace: "Alamu ne garemu, za mu iya bibiyarta har mu isa gida a yayin da muka bace yayin yaki.

"A shekaru 300 da suka gabata tun zamanin kakanninmu, an ce tana da matukar amfani don suna bauta mata. Har yau muna bauta mata." Ahenenanhene Osae Adade, ya zarga cewa a duk lokacin da suka kwanta bacci, Mpeni Kofi na zagayawa garin a siffar dogon mutum don basu kariya.

Shugabannin sun yarda cewa bishiyar na da wata babbar alaka ta musamman da fadar Okuaphene kuma ita ke hada kawunan jama'ar da ke gidajen da ke zagaye da ita. A wani labari na daban, shugaba bature daya aka taba yi a kasar Zambia kuma sunansa Peter Fisher, wanda aka sani da Chief Nyamwana. Ya jagoranci kabilar yankin Mwinilunga da ke Zambia.


SOURCE: LEGIT.NG

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Duba Bishiya mai shekaru 300 da ake zargin tana komawa mutum tsakar dare "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?