--
Illolin karas 5 a jikin ɗan adam da ya kamata ku sani da ya dace ku sani

Illolin karas 5 a jikin ɗan adam da ya kamata ku sani da ya dace ku sani





Idan ana magana a kan abinci masu inganta lafiya, mafi yawancin lokuta ganye da kayan lambu suna daga cikin wadanda aka fi ambatta kamar yadda binciken kimayya da likitoci suka gano.

Sai dai duk da dimbin amfanin da ke tattare da kayan lambun wasu lokutan akwai wasu illoli da mutane da dama ba su san da su ba.

Hakan yasa za mu lissafa tare da yin takaitattun bayani a kan wasu illoli da cin karas ka iya kawo wa ga jikin dan adam kamar yadda The Guardian ta wallafa.

1. Yana dauke da sukari mai dimbin yawa

Ya kamata mutane da ke da cutar sukari da aka fi sani da diabetes su yi taka tsan tsan game da cin karas domin yana dauke da sukari mai yawa.

Jikin dan adam na sauya sukarin da ke cikin karas zuwa glucose wanda shi kuma ke kara adadin sukarin da ke jinin dan adam cikin gaggawa.

Idan ya zama dole mai ciwon diabtes zai ci karas, ya fi dace wa ya dan dafa karas din kuma ya ci kadan.

2. Ya kan janyo cutar Carotenemia

Karas na dauke da sinadarin beta carotene wanda jikin dan adam ke sauya ta zuwa Vitamin A. Cin karas fiye da kima ya ka saka sinadarin carotene ya yi yawa a jinin mutum sai ya janyo cutar Carotenemia wacce ke saka fatar mutum ta koma launin ruwan dorawa.

3. Ya kan janyo kurarraji, gudawa da 'borin jini'

Akwai wasu mutane da jikinsa baya son karas, idan sun ci karas din su kan game da matsaloli kamar kurarraji a fatarsu, gudawa, kaikayin jiki, kumburin jiki da sauransu.

Akwai wata sinadari da ke tayar janyo wannan matsalar da ake samu a ganyen karas din.

4. Ya kan yi wa jarirai illa

Wasu bincike da masu nazarin kimiyya suka gudanar ya nuna cewa bai dace a rika bawa kananan yara karas ba. Hakan yasa idan ya zama dole sai dai a bawa yara dan kadan.

5. Karas na canja dandanon nonon mai shayarwa

A lokacin da mace ke shayarwa, duk abinda ta ci ya kan sauya dandadon ruwan nonon ta. Ya kamata mata masu shayarwa su takaita cin karas domin bincike da dama sun nuna karas na canja dandanon nonon mai shayarwa.


SOURCE: LEGIT.NG

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Illolin karas 5 a jikin ɗan adam da ya kamata ku sani da ya dace ku sani"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?