--
Abin takaici ne haka uwargidata ke son ganin bayana - Mutumin da matarsa ta yankewa azzakari

Abin takaici ne haka uwargidata ke son ganin bayana - Mutumin da matarsa ta yankewa azzakari



Ranar Talata, 30 ga Yuni, 2020, wata rana ce da Aliyu Umaru, ba zai taba mantawa ba a rayuwarsa saboda a wannan rana uwargidarsa, Halima, ta guntule masa azzakari da wuka.


Yana kwance yanzu a asibiti cikin radadin jiki da zuciya a asibitin koyarwan gwamnatin tarayya dake Gombe, inda aka kaisa bayan aukuwan hadarin.


A asibitin, an ga yadda Likitoci suka sanya masa na'ura na musamman domin taimaka masa wajen fitsari yayinda aka ajiye azzakarinsa da matar ta yanke gefe guda cikin leda. A hirar da jaridar Punch tayi da shi, Aliyu Umar ya bayyana irin iftila'in ya shiga ciki.

Yace: "Ni dillalin Likitocin dabbobi ne. Ina sayar da magungunan dabbobi. shekaru na 42 kuma ina da mata biyu da yara biyu." "Ni mazaunin garin Tella ne a karamar hukumar Gassol a jihar Taraba.



An turo ni asibitin koyarwan tarayya Gombe ne daga FMC Taraba." "Bayan dawowa na daga aiki, na debi ruwa don yin wanka kuma na ci abincin da iyalina ta girka kuma nayi bacci. Daga baya wani mugun azaba ya tasheni daga barci ina iwu."


"Uwargidata ta yanke min 'bura'. A lokaci aka sanar da makwabta. Ban sani ba (akwai yiwuwan) an sanya magani cikin abincin saboda yadda nayi bacci mai zurfi. Matata ta lalata min rayuwa kuma akwai takaici."

Rahotanni sun nuna cewa Halima ta kasance cikin takun tsaka da mijinta da kishiyarta. Dan'uwan Umaru, Malam Usman ya bayyana cewa yana gidansa cikin dare aka kirashi a waya cewa akwai matsala.


Yace: "Cikin dare wayata ta fara kara, ashe yayana. Ya fada min abinda ya faru da shi. Da wuri aka garzaya da shi FMC Taraba domin tsayar da jinin dake kwarara da kuma yi masa tiyata."


"Amma suka kasa yin aikin saboda sun ce basu da isasshen kayan aiki. Sai suka bamu shawaran kai shi wani asibitin daban." "Ita kuma mun fadawa mutane kada wanda ya taba ta. Aikin gama ya gama kuma babu yadda zamuyi. Mun barta da Allah. Babu abinda zamuyi mata da zai dawo da azzakarin 'danuwana."



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Abin takaici ne haka uwargidata ke son ganin bayana - Mutumin da matarsa ta yankewa azzakari"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?