LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Zamfara: Matashi ya yi wa matar yayansa fyade daga bisani ya kasheta

ROHOTON: LEGIT.NG

Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da kama wani matashi mai suna Aminu Bala mai shekaru 25 a duniya sakamakon zarginsa da yi wa matar yayansa fyade da kasheta a Gusau. Mai magana da yawun rundunar, SP Mohammed Shehu yayin kama wanda ake zargin a ranar Litinin, ya ce tuni Bala ya amsa laifinsa.

Shehu ya ce wanda ake zargin dan asalin kauyen Damaga ne da ke karamar hukumar Maradun ta jihar. Ya ce, "Ofishin 'yan sanda da ke Tudun Wada Gusau ta samu kiran gaggawa wurin karfe 4:30 na yammacin ranar 15 ga watan Yuni. Ta samu kiran daga kwatas din Damba a tsakiyar birnin Gusau inda wanda ake zargin ya kashe matar yayansa. "Yan sandan sun hanzarta zuwa wurin da abun ya faru tare da samun gawar Hauwa Iliyasu a cikin jini bayan raunikan da ta samu sakamakon yankan adda.

"An mika ta asibitin kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta." Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce an tuntubi mai gidan matar mai suna Kabiru Bala ta wayar tarho. "Baya jihar amma ya sanar da 'yan sanda cewa Aminu ya taba barazanar kisa ga matarsa," yace. Shehu ya ce rundunar tana jiran isowar mijin mamaciyar domin samun bayaninsa wanda za a mika gaban kuliya. Hauwau ta rasu ta bar yara biyu, daga ciki akwai yaro mai watanni tara da take goyo.

A wani labri na daban, tsintar gawar manomi ce ta janyo zanga-zanga a kananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf. Wannan al'amarin ne yasa gwamnatin jihar ta saka dokar ta-baci ta sa'o'i 24, jaridar Daily Trust ta gano.

Majiya daga jami'an da kuma mazauna yankin ta sanar da cewa matasan kabilar Hausa da na Kataf ne suka yi arangama a kan gona wacce dukkan kabilun ke ikirarin nata ne. A yayin arangamar, matasa uku sun raunata kafin dattawan yankin su shiga tsakani don gujewa irin rikicin watan Fabrairun 1992 da na Mayu da aka yi a garin Zangon Kataf.

Amma kuma abinda ya kawo rikicin ranar Alhamis da ta gabata shine kisan Yusuf Musa, dan asalin Kauru amma yana zama a Zangon Kataf inda mahaifinsa yake. Majiya daga jami'an tsaro wacce bata bari a ambaceta ba, ta ce an kashe marigayi Musa ne a gona kuma ganin gawarsa ne ya kawo zanga-zanga tsakanin garin Zango da Bakin Kogi kusa da karamar hukumar Kauru.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments