LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

A karshe dai an saki babban Dogarin Aisha Buhari, wanda rikici ya hado shi da dan uwan shugaba Buhari

Yanzu-yanzu an saki babban Dogarin Aisha Buhari, Usman Shugaba, wanda aka tsare a ofishin ‘yan sanda makon da ya gabata bayan rikici ya hado shi da dan uwan shugaba Buhari, Sabiu Yusuf.

Sabiu Yusuf, wanda ya rike mukamin mai taimakawa shugaban kasar na musamman, an ruwaito cewa ya taso daga Legas zuwa Abuja a ranar 8 ga watan Yuni, inda ya wuce kai tsaye zuwa fadar shugaban kasa, inda yake zaune, amma yana zuwa sai Shugaba da sauran Dogaran Aisha Buhari suka hana shi shiga, inda suka ce sai an killace a wani wuri tunda har daga jihar Legas ya fito, inda take ita ce jihar da tafi ko ina yawan masu cutar COVID-19 a Najeriya.

Sabiu yaki yadda, inda ya sanya ‘yan sanda suka kama Shugaba da sauran masu taimakawa Aisha Buhari.

A ranar Juma’a 12 ga watan Yuni, Aisha Buhari ta wallafa wani rubutu a shafinta na Twitter, inda ta bukaci a sakar mata ma’aikatan nata.

A yadda wata majiya daga fadar shugaban kasar ta bayyana, an saki Shugaba a safiyar ranar Litinin 15 ga watan Yuni, inda kuma aka canja masa wajen aiki zuwa helkwatar tsaro dake babban birnin tarayya Abuja.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a fannin sadarwa, Malam Garba Shehu, ya saki wata sanarwa a cikin karshen makon da ya gabata, inda ya bayyana cewa tuni an fara bincike akan wannan lamari.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments