--
Za mu kalubanci Gwamnatin Shugaba Buhari a kan batun IPPIS – Kungiyar ASUU

Za mu kalubanci Gwamnatin Shugaba Buhari a kan batun IPPIS – Kungiyar ASUU



ROHOTON: LEGIT.NG

Kungiyar Malaman jami’a ta ASUU, ta zargi gwamnatin tarayya da kwakwulo bayanai game da lambobin ‘ya ‘yanta na BVN ta karkashin kasa domin a jefa su cikin tsarin IPPIS.

Shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi ya ce gwamnatin Najeriya ta yi wannan aiki ne da nufin a kakaba malaman jami’o’i a karkashin tsarin biyan albashi na IPPIS ta bayan fage.

Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayyana cewa za su kalubalanci matakin da gwamnati ta dauka domin hakan ya sabawa dokokin babban bankin Najeriya na CBN game da BVN.

Biodun Ogunyemi ya ce CBN ta haramtawa kowa samun bayanai game da lambar mutum ta BVN ba tare da izninsa ba. Shugaban ASUU ya bayyana wannan a hirarsa da Vanguard.

Ogunyemi ya ce gwamnati ta bukaci ‘yan ASUU su bada lambobinsu na BVN kafin a biya su albashin Fubrairu da Maris, amma malaman jami’an su ka ki bin wannan umarni.

“Abin da gwamnati ta ya sabawa doka, kuma laifi ne. Lokacin da su ka gana da mu kan albashinmu na Fubrairu da Maris, bayan tattaunawa sun yarda za su biya mu kudinmu.”

“Sun bukaci mu bada lambar asusun bakinmu. Mun yi mamaki da mu ka ji cewa sun je su na neman lambobinmu na BVN. Za mu yi ta da su a kan wannan.” Inji Biodun Ogunyemi.

“Babu dalilin yin wannan. Sun yi aikin banza. Su na tunanin za su iya jefa mu cikin IPPIS ne ta karkashin kasa." Shugaban na ASUU ya ce: “Ba mu canza matsayarmu kan IPPIS ba.”

A game da tsarin IPPIS, shugaban na ASUU ya ce manhajar ba za ta yi wa jami’o’i aiki ba saboda yadda makarantun su ka sha banban. ASUU ta ce IPPIS ta na zaftare albashin ma’aikata.

“Kuskure ne a dauka IPPIS ne kadai sabanin ASUU da gwamnati, asali ma an kawo lamarin ne domin a kauda tunanin jama’a. Akwai batutuwan da sun fi karfin wannan.” Inji Farfesan.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Za mu kalubanci Gwamnatin Shugaba Buhari a kan batun IPPIS – Kungiyar ASUU"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?