--
Diezani Alison Madukwe ta zama Kwamishina a kasar Dominican Republic

Diezani Alison Madukwe ta zama Kwamishina a kasar Dominican Republic



ROHOTON: LEGIT.NG

Rahotanni sun fara bayyana a game da yadda tsohuwar ministan man Najeriya, Madam Diezani Alison-Madueke ta lallaba ta tsere daga Najeriya a daf da karshen mulkin Goodluck Jonathan. Diezani Alison-Madueke wanda ake zargi da laiffufuka a Najeriya, ta samu takardar fasfo da ake ba manyan ‘yan kasa a hannun gwamnatin Dominican Republic bayan ta sauka daga kan mulki. Jaridar Pulse ta ce bayan samun fasfo,

 Alison-Madueke wanda ta rike kujerar ministar mai a gwamnatin PDP tsakanin 2010 zuwa 2015, ta zama Kwamishina a kasar Dominican Republic. Wasu takardu da su ka fito daga hukumar su ka fada hannun jaridar Pulse sun nuna cewa Diezani Alison-Madueke ta samu mukamin kwamishinar kasuwanci da hada-hada a kasar wajen. Wani jami’in hukumar EFCC ya shaidawa jaridar cewa “Da wannan fasfo na musamman, (Diezani) ta samu Katanga daga damkar kowace hukuma da jami’an tsaro, har da Interpol.”

Ya ce: “Kafin barin ofis a ranar 28 ga watan Mayu, 2015, ta shawo kan ta da Firayim Ministan kasar Dominica. Ta shiga-ta fita, aka nada ta Kwamishinar kasuwanci da kuma hada-hada.” Alison-Madueke ta dare kan wannan kujera ne a ranar 1 ga watan Yuni, 2015. Kutun-kutun din da ta yi ya yi aiki, wata wasika da ta fito daga ofishin Firayamin Ministan kasar ta tabbatar da haka. Majiyar ta ce “Bayan Firayim Minista Roosevelt Kerry ya ba Diezani Alison-Madueke takardar zama cikakkar ‘yar kasa, ya kuma ba ta kujerar Kwamishinar kasuwanci da zuba hannun jari.”

 Da wannan takardu da fasfo har jami’an kasar Amurka ba su da hurumin cafke tsohuwar ministar Najeriyar. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, takardun za su tashi aiki ne a cikin Mayun 2020. A shafi na 32 na fasfon da aka ba Alison-Madueke, an bayyana ba ya halasta a kama ta. Haka zalika duk wanda ya mallaki wannan takarda zai zamu alfarma a duk kasar da ya samu kansa.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Diezani Alison Madukwe ta zama Kwamishina a kasar Dominican Republic "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?