LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Za mu hukunta duk Malamin Islamiyyar da ya bude makaranta – Gwamnatin jihar KanoA wata hira da kwamishinan ilimi na jihar Kano, Sunusi Maji Dadin Kiru, yayi da da gidan rediyon vision dake jihar, ya bayyana cewa gwamnatin jihar baza ta sassautawa duk wanda ta kama ya karya dokar bude makarantu ba.

Kwamishinan ya bayyana hakane a lokacin da yake amsa tambayoyi game da batun komawa makaranta, inda ya ce za su hukunta duk wani Malamin Islamiyya da aka kama shi da hannu wajen bude makaranta a fadin jihar.

Ya ce bude makarantun islamiyyoyi a wannan lokacin zai sanya rayuwar mutane musamman ma ta daliban cikin hadari, inda yayi gargadi ga Malaman akan kada su sake su bude makaranta har sai gwamnatin jihar ta basu dama.

Ya ce: “Duk wanda muka kama da hannu wajen karya dokar da muka sanya za mu dauki hukunci a kansa mummuna.”

A daya bangaren kuma gwamnatin tarayya tayi gargadi ga gwamnonin jihohi akan suyi watsi da matsin lambar da iyayen yara suke saka musu wajen bude makarantu.

Gwamnatin tace ba karamin hatsari bane a bari daliban su koma makaranta a wannan lokacin, inda ta ce amma daliban da suke shirin zana jarrabawar WAEC da NECO lokaci na nan zuwa da za a barsu su koma makarantu.

 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments