LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Mutuwar kasko: Miji ya soka wa matarsa wuka sannan ya sha gubaWani mutum dan Najeriya me zama a Victory Park Estate da ke Lekki a jihar Legas, ya kashe kansa bayan ya sokawa matarsa wuka har lahira. Bala Elkana, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga The Cable Lifestyle a ranar Litinin, ya ce an adana gawawwakin mamatan a ranar Lahadi.

Ya ce a lokacin da 'yan sandan suka isa wurin da abun ya faru, kumfa ce ke fita daga bakin mutumin, lamarin da ke nuna cewa guba ya sha. Matarsa kuwa na kwance a cikin jininta. Elkana ya ce an dauke wukar wacce ake tunanin an yi amfani da ita wurin kashe matar tare da kwalaben Sniper, wanda ake tsammanin ya yi amfani da shi wurin kashe kansa. Kakakin ya kara da cewa, yayin da ake binciken yadda lamarin ya auku, ana tsammanin mutumin ya soka wa matarsa wuka sannan ya kashe kansa daga baya

"Zan iya tabbatar muku da aukuwar lamarin. Mun mika gawawwakin asibiti don gwajin abinda ya kasheta. Mun ganta a cikin jini," Elkana ya sanar da The Cable Lifestyle. "Wukar yanka ce aka samu a wurin tare da kwalbar sniper biyu wacce ake tsammanin ya sha domin kumfa ce ke fita daga bakinsa.

"Likitoci za su gano silar mutuwarsu duk da hasashe a yanzu na nuna cewa ya kasheta ne sannan ya kashe kansa. Ana ci gaba da bincike," yace. Amma kuma har yanzu ba a gane abinda ya kai mutumin da yin wannan aika-aikar ba.KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments