--
Yanzu-yanzu: Wani gwamna ya sake kamuwa da cutar Coronavirus

Yanzu-yanzu: Wani gwamna ya sake kamuwa da cutar Coronavirus



ROHOTON: LEGIT.NG

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa gwamnan jihar Abiya, Okeazie Ikpeazu, ya kamu da cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus. Kwamishanan labaran jihar, John Okiyi Kalu,

ya sanar da hakan a jawabin da ya saki ranar Litinin, TheCable ta ruwaito. Ya ce tuni gwamnan ya killace kansa tun kafin sakamakonsa ya fito kuma ya umurci mataimakinsa ya dane kujerarsa kafin ya samu sauki

Yace: "Za ku tuna cewa a ranar Asabar, 30 ga watan Mayu 2020, gwamna Okezie Ikeazu, ya bayar da samfurinsa domin gwaji kuma ya umurci mambobin majalisar zartarwarsa da mambobin kwamitin yaki da cutar su bada nasu domin gwaji."
Gwamnan Abiya Source: Depositphotos 

"A ranar Talata, 2 ga watan Yuni, 2020, sakamakon gwamnan ya fito kuma bai kamu da cutar ba. Amma ranar 4 ga Yuni, 2020, gwamnan ya sake bada samfurinsa a dakin gwajin NCDC domin tabbatarwa kuma sai ta dawo ya kamu."

"Saboda haka, Gwamna Okezie Ikpeazu, ya killace kansa kamar yadda sharrudan NCDC ya bukata kuma kwararrun likitoci na dubashi." "Saboda haka, gwamnan ya umurci mataimakinsa, Ude Oko Chukwu, ya zama mukaddashin gwamna kafin ya dawo bakin aiki." "Muna kira ga al'ummar jihar Abiya su dau wannan yakin da COVID-19 da gaske saboda gaskiya ne."

Za ku tuna cewa hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 260 a fadin Najeriya. Jihar Abiya ce ta zo na daya da sabbin masu cutar 67, sannan birnin tarayya Abuja 40.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.49 na daren ranar Lahadi 7 ga Yuni na shekarar 2020. Alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar Lahadi 7 ga Yunin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 12486. An sallami mutum 3959 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 354.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu-yanzu: Wani gwamna ya sake kamuwa da cutar Coronavirus "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?