--
Dokar kulle: Gwamnatin jihar Kano ta rufe manyan Otal guda biyu

Dokar kulle: Gwamnatin jihar Kano ta rufe manyan Otal guda biyu



ROHOTON: LEGIT.NG

Wata kotun tafi da gidanka da ke karkashin mai sharia'a, majistare Aminu Gabari, ta bayar da umarnin rufe wasu manyan Otals guda biyu da ke birinin Kano. Gabari ya bayar da umarnin rufe manyan Otals guda biyu na tsawon wata shidda bayan samunsu da laifin karya dokar kulle da aka saka a jihar Kano sakamakon bullar annobar korona.

Manayan Otals din da kotun mai lamba ta biyar ta rufe a karshen makon nan sune kamar haka; Mozida Otel da ke No-Man's Land da Otal din Royal Tropicana da ke kan titin Zungeru a unguwar Sabon Gari. Jami'an tsaron hadin gwuiwa da ke aikin tabbatar da biyayya ga dokar kulle sun kai samame Otals din a daren ranar Juma'a,

inda suka kama dumbin mutanen da suka gani suna harkokinsu a harabar Otal din. A ranar Asabar rundunar 'yan sanda ta gurfanar da kusan mutane 50 da aka kama a gaban kotun tafi da gidanka bisa tuhumarsu da laifin karya dokar zaman gida da gwamnatin jihar ta saka.

Kotun ta ci kowanne mutum daga cikin mutanen tarar N20,000 tare da saka su aikin share manyan titunan birnin Kano na tsawon wata biyu. Dukkan mutanen sun amsa cewa sun aikata laifin da ake tuhumarsu da shi.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Dokar kulle: Gwamnatin jihar Kano ta rufe manyan Otal guda biyu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?