LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta rage farashin man fetur zuwa N121.50ROHOTON: LEGIT.NG

Gwamnatin tarayya ta rage farashin litan mai a fadin Najeriya zuwa N121.50 sabanin N125.00 da ake sayarwa yanzu. Hukumar duba farashin man fetur PPPRA ta yi sanarwa ne a wasikar da ta aikewa yan kasuwar mai a ranar Lahadi, 31 ga Mayu, 2020. Daily Trust ta ruwaito cewa an rage farashin man feturin ne sakamakon faduwar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya da annobar COVID-19 ta haifar.

Wannan shine karo na uku da za'a rage farashin man fetur cikin nan ta shekarar 2020. A ranar 18 ga Maris, gwamnatin tarayya ta sanar da ragin farashin litan mai daga N145 zuwa N125. Daga baya a ranar 31 ga Maris, an sanar da karin ragi daga N123.50 zuwa N125.00.

Duk da cewa gwamnatin tarayya ta rage farashin zuwa N123 a watan Mayu da ya gabata, yan kasuwar mai da gidajen mai basu rage farashin ba, N125 suka cigaba da sayarwa. Yan Najeriya na tsoron da yiwuwan yan kasuwan mai su kara kunnen kashi ga wannan ragi kamar yadda sukayi a watan jiya.

Farashin danyen man fetur ya yi fadin da ba a taba tsammani ba yayinda cutar Korona ta addabi duniya. Kawo yau, farashin ganagar danyen man fetur a kasuwar OPEC $29.4 ne. Kuma sanannen abu ne cewa idan farashin mai ya ragu a kasuwar duniya, kudin tacaccen mai zai ragu a nan gida Najeriya.

 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments