LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yanzu-yanzu: An dage gasar AFCON ta 2021 saboda korona

Kwamitin zartarwa na Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka, CAF, ta dage gasar cin kofin Afirka ta shekarar 2021 zuwa 2022 domin annobar coronavirus. Taron da a baya aka shirya yi a watan Janairun shekarar 2021 yanzu an dage shi zuwa shekarar 2022 kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Hukumar ta bayar da sanarwar ne bayan taron da yan kwamitin suka gudanar da bidiyo a ranar Talata inda suka tattauna batutuwan da suka shafi gudanar da gasar a yanayi irin ta annobar COVID-19.

"Bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kan halin kallubalen da duniya ke fuskanta, an dage gasar zuwa watan Janairun shekarar 2022," kamar yadda sanarwar ta CAF ta ce. "Za a sanar da ranakun da za a karasa buga wasannin karshe wadanda za su samu nasarar buga gasar a nan gaba."

Ku saurari karin bayani ...  SOURCE: LEGIT.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments