--
Yanzu aka fara annobar korona a Najeriya – PTF

Yanzu aka fara annobar korona a Najeriya – PTF

ROHOTON: LEGIT.NG

Kwamitin yaki da COVID-19 ta shugaban kasa, PTF ta ce akwai yiwuwar yanzu ne annobar korona ta fara yaduwa a Najeriya. PTF ta koka kan yadda yan Najeriya suke gudun zuwa yin gwajin wadda hakan yasa har yanzu mutane kalilan aka yi wa gwajin idan aka kwatanta da adadin mutanen da ke kasar.

An sanar da hakan ne yayin da mambobin PTF suka bayyana a gaban kwamitin hadaka ta majalisar wakilai da dattijai domin yi musu bayani kan yadda aka kashe kudaden da aka bawa Najeriya tallafi don yaki da corona. Shugaban PTF, kuma sakataren gwmanatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana fargabansa kan rashin sanin yadda annobar za ta kasance inda ya roki 'yan majalisar su taimaka wurin wayar da mutane a mazabansu.

Ya ce, "Wannan kwayar cutar na da hatsari sosai. Har yanzu ba mu tsira ba, ya zama dole mu yi shiri. Ba mu san lokacin da cutar za ta tafi ba, hakan yasa ba mu kashe dukkan kudaden da aka bamu ba. "Ba mu san tsawon lokacin da zamu magance cutar ba. Ko kasafin kudin da shugaban yaki da annobar na kasa ya bayar na watanni shida ne. Amma da izinin Allah za muyi nasara. "Babu magani ko riga kafi. Lamarin ya jefa mutane cikin damuwa.

Komai ya rikice. Yau gashi duk mun saka takunkumi. Ba haka muka saba ba. "Akwai taimakon da za ku iya mana. Akwai dokoki da za a iya yi saboda gaba. Muna yaki da cutar a yanzu, bai dace mu bari wata annobar ta zo ba mu shirya ba. Ya zama dole muyi shiri." Da fari, shugaban NCDC, Ihekweazu ya karyata jita jitar da ake yadawa na cea hukumarsa ta kashe miliyoyin naira wurin aike wa da sakon kar ta kwana na wayar da kan 'yan Najeriya. Ya ce,

"Labarin sakonnin sakon tes karya ne. Ba zai yiwu mu kashe irin wannan kudin ba. Hasali ma, dukkan sakon da aka aike wa kowa kyauta ne daga kamfanonin sadarwa a kasar. "Ba mu biya ko sisi ba domin sakon kar ta kwana. A halin yanzu mutanen da muka yi wa gwaji ba su kai 100,000 ba. A halin yanzu muna da kayan aikin yi wa mutum fiye da 200,000 gwaji."

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu aka fara annobar korona a Najeriya – PTF "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?