--
Al-ajabi: Uwar 'ya'ya 13 ta haifi 'yan hudu a Zaria

Al-ajabi: Uwar 'ya'ya 13 ta haifi 'yan hudu a Zaria

ROHOTON: LEGIT.NG

Wata matar aure, Hauwa'u Sulaiman, wacce ke zaune a gida mai lamba 70 a unguwar Alfadarai da ke Zaria, ta haifi 'yan hudu a babban asibitin Gambo Sawaba da ke garin Zaria. Kafin haihuwar 'yan hudun a ranar Juma'a, 5 ga watan Yuni, Hauwa'u ta haifi yara 13 a baya. Yayin hirarta da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Talata, Hauwa'u ta ce yanzu tana da 'ya'ya 17 daga haihuwa takwas da ta taba yi.

An mayar da Hauwa'u da jariranta zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zaria domin samun kyakyawar kulawa. Hauwa'u ta ce jariri daya namiji daga cikin 'yan hudun da ta haifa ya mutu kafin su karasa asibitin ABUTH Ta ce ragowar jarirai uku na bangare na musamman domin kulawa da kananan yara a yayin da ita kuma take samun kulawa a bangaren karbar haihuwa na asibitin.

Ta kara da cewa sai da aka kara mata jini leda biyu yayin da take haifar jariran. "Ina cikin koshin lafiya da karfin jiki, amma ma'aikatan lafiya sun bani shawarar na cigaba da hutawa a asibiti domin su saka ido a kaina kafin su sallameni,"

a cewar Hauwa'u. Mijin Hauwa'u, Sulaiman Mohammed, ya ce matar tasa ta taba haihuwar 'yan uku har sau biyu, tagwaye sau biyu, da kuma haihuwar dai - dai sau uku, a baya kafin ta haifi 'yan hudu yanzu. Sulaiman, mai sana'ar tukin mota, ya ce dan uwansa ya ke taimaka masa a kan harkar yaransa duk lokacin da bukata ta taso.

Kazalika, Saudatu Haruna, mahaifiyar Sulaiman ta ce bata yi mamakin cewar Hauwa'u ta haifi 'yan hudu ba. Ta alakanta abin da gado tare da bayyana cewa sau uku tana haifar tagwaye a lokuta daban - daban. Saudatu ta kara da cewa a cikin 'yan uku aka haifi mahaifiyarta, sannan mahaifinta tagwaye ne, a saboda haka haihuwa 'yan hudu a zuri'arta ba zai zama abin mamaki ba. Dakta Isa Abdulkadir, babban likita a bangaren yara a asibitin ABUTH, ya ce ragowar jariran uku suna cikin koshin lafiya.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Al-ajabi: Uwar 'ya'ya 13 ta haifi 'yan hudu a Zaria"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?