--
Yadda kawuna dan Boko Haram ya dinga lalata dani a matsayin ganima

Yadda kawuna dan Boko Haram ya dinga lalata dani a matsayin ganima



ROHOTON: LEGIT.NG

Bayan majalisar dinkin duniya ta ware ranar 19 ga watan Yunin duk shekara don yaki da cin zarafi, wata baiwar Allah da ta bukaci a boye sunanta ta shaida wa BBC cewa "'yan Boko Haram sun ci zarafinmu inda suka dinga lalata da mu." Matashiyar ta sanar da cewa wannan lamarin ya auku ne a lokacin da mayakan ta'addancin Boko Haram suka kai hari garinsu. A cewarta,

"Mayakan sun shigo garinmu a ranar wata Talata suna kabbara har suka karbe garin. Sun kashe dukkan maza sannan suka kada matan." Ta kara da cewa "ranar wata Talata sai 'yan Boko Haram suka shigo garinmu suna kabbara inda suka karbe garin suka kuma kashe duk maza sannan sai suka kada duk mata zuwa daji bayan sun kone garin.

"A wannan ranar kawuna ya zo wanda kanin mahaifina ne, ya ce in bishi na zama ganimar yaki. Daga nan ya tafi dani ya dinga saduwa da ni." Matashiyar ta ci gaba da cewa, "Daga bisani aka samu daya daga cikin wadanda suka kashe mahaifina aka aura masa ni. "Na samu guduwa daga hannunsa a wani dare da misalin karfe daya saboda a wannan lokacin suna bacci."

Kamar yadda matashiyar ta bayyana, duk da tserewar da suka yi daga hannun 'yan Boko Haram, tana fuskantar tsangwama da cin zarafi a sansanin 'yan gudun hijira da ke Bama. Ta kara da cewa, "Duk wurin da muka bi ko muka zauna a sansanin, sai a dinga nuna mu ana cewa ga matan 'yan Boko Haram. "A gaskiya ba zan taba yafewa ba a kan abinda Boko Haram ta yi min ballantana kawuna wanda ya dinga lalata da ni. Allah ya isar min."

Daga bisani, matashiyar ta samu komawa makarantar Boko inda tace tana fatan zaman sojar sama don yakar Boko Haram. "Burina a halin yanzu shine zama sojan sama domin in yi amfani da jirgi don wargaza Boko Haram. Ina fatan ganin bayan Boko Haram a Najeriya," in ji matashiyar. A halin yanzu tana makaranta sannan tana koyon sana'ar dinki a wata cibiyar agaji ga masu gudun hijira.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yadda kawuna dan Boko Haram ya dinga lalata dani a matsayin ganima"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?