LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

A sa ran cewa COVID-19 za ta cigaba da ta’adin kashe Bayin Allah – GwamnatiROHOTON: LEGIT.NG

Ministan harkokin kiwon lafiyan Najeriya, Osagie Ehanire, ya ce karuwar masu dauke da Coronavirus da ake samu a kasar nan, alama ce ta cewa za a samu karin mutanen da za su mutu.

Dr. Osagie Ehanire ya yi wannan gargadi ne a babban birnin tarayya Abuja kamar yadda jaridar Daily Trust ta bada rahoto a ranar Juma’a, 19 ga watan Yuni, 2020.

Da ya ke jawabi a lokacin da kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar COVID-19 ta zanta da ‘yan jaridar, Miinistan ya ce sun dauki mataki na rage adadin wadanda cutar COVID-19 za ta kashe.

Ya ce: “Tun da mafi yawan wadanda su ke mutuwa, mutanen da su ka haura shekara 50 ne da haihuwa, ko kuma masu fama da wani rashin lafiya kamar ciwon sukari, kansa, hawan jini, ciwon koda, kanjamau da sauransu, rukunan wadannan mutane su na samun kariya ta musamman.”

“Shiga wuraren da za a samu cinkoso kamar kasuwa ko wuraren ibada ya na da hadari, haka zama a cikin killataccen daki ga mutum a kadaice, ya na kara barazanar kwayar cutar.”

A dalilin haka tsofaffi da masu larura bai kamata su killace kansu a daki musamman cikin dare ko a lokutan da babu kowa ba, domin cutar ta na iya bude mutum farat daya ba tare da an kawo agaji ba, inji Enahire.

Ministan ya kara da cewa: “Duk wanda gwaji ya nuna ya na dauke da cutar, ya kuma cigaba da zama a gida ko wani wuri, ayi maza a kai shi wurin jinya da zarar ya fara gaza numfashi.”

“Jinkiri ya na iya kawo babbar matsala, cutar ta na iya yin kamari a cikin lokacin da ba ayi tunani ba.” Ya ce: Wannan bakuwar cuta ta na cikinmu, ta na kama mutane kullum a cikin al’umma.”


Shugaban kula da wannan kwamiti na kasa, Dr. Sani Aliyu ya shaidawa jama’a cewa wannan annoba ba ta kama hanyar zuwa karshe ba, ya ce akwai karin yiwuwar mutane su kamu da cutar a yanzu.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments